Man fetur na Nijeriya ne ba Neja Delta ba –Obasanjo

Cif olusegunObasanjo
Daga Mahmud Gambo
Sani Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce, man fetur da ma sauran albarkatun kasar na dukkan ‘yan Nijeriya ne. Ya bayyana haka ne a wani martani da ya mayar wa fitaccen dattijon nan na yankin Neja Delta, Cif Edwin Clark, wanda ya zargi Obasanjo da nuna halin ko-in-kula game da illolin da hakar mai a yankin nasu ta haddasa.
Rahotanni sun ambato Clark, a cikin wata wasika da ya rubuta, yana zargin tsohon shugaban kasar da nuna kiyayya ga masu fafutukar mallakar albarkatun kasa da aka samu a yankunansu.
Sai dai a martanin da ya mayar, Obasanjo ya ce, a iya saninsa albarkatun kasa da aka hako a Nijeriya mallakin dukkan ‘yan kasar ne ba na mutanen yankunan da aka same su ba.
Ya kara da cewa, ba zai yiwu a samu kasashe biyu a cikin kasa daya ba, yana mai cewa, a iya fahimtarsa Cif Clark yana magana ne a kan samar da wata kasa a cikin Nijeriya idan har yana so a bai wa Neja Delta damar mallakar albarkatun kasa da aka samu a yankin.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya yarda cewa, zinaren da aka samu a Zamfara, ko zinaren da aka samu a Ilesha da ke jihar Osun, ma’adinin lead da ke jihar Ebonyi shi ne kuma ya bayyana cewa, fetur da aka samu a Neja Delta duka na ‘yan kasar ne.
Tsohon shugaban ya ce, dukkan mutanen da suka kulla yarjejeniyar sayen danyen man fetur sun yi ne da Nijeriya a matsayin kasa ba da yankin Neja Delta ba, yana mai jaddada cewa, Nijeriya dunkulalliyar kasa ce, da babu wanda ya isa ya raba ta, ciki har da rarraba albarkatun da ke cikinta. A cewarsa: “Idan akwai wata barazanar tsaro a kowane bangare na Nijeriya a yau, ciki har da yankin Neja Delta, sojojin Nijeriya ne tare da tallafin wadansu jami’an tsaro, a matakin gwamnatin tarayya, za su yi raddi kan hakan.”
Masu fafutuka a yankin Neja Delta sun dade suna kokarin ganin sun mallaki man fetur da ake hakowa a yankinsu, inda a wadansu lokutan lamarin yakan kai ga kashe-kashen rayuka da satar ma’aikatan man fetur.