Man kara girman nono na jawo kansa -In ji Maryam Abubakar

Man kara girman nono na jawo kansa -In ji Maryam Abubakar

Man kara girman nono na jawo kansa

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe

Yawan Shafe-Shafen  mai domin kara girman nono na mata yana jawo kansar nono in ji ma’aikatar lafiya.

Malama Maryam Abubakar, kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce a babban asibitin gwamnati na jihar Jigawa da ke babban birnin jihar Dutse, ita ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Gombe.

Maryam Abubakar, ta ce, kuskuren da wadansu mata ke yi shi ne suna shafa mayuka domin kara girman nononsu domin su burge maza, ba tare da sanin illar hakan ba shi ne ke jawo masu cutar daji watau kansa.

Ta yi kira ga matan da suke da irin dabi’ar da cewa, su gujewa hakan domin samun lafiyarsu.

Ta kuma kara da cewa, kamar mata masu ciki a jihar Jigawa ana ba su kulawa ta musamman wajen ganin an ceto lafiyarsu tare ba su gidajen sauro da magunguna na kariya daga kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kuma zubewar ciki.

Alamon Sankara

Maryam Abubakar, ta ce, idan mace ta gwada nonon ta taji akwai wani gullutu ko ta matsa bakin nonon ta ga wani ruwa kalar rawaya watau yellow to akwai alamar sankara sai taje asibiti a bata magani.

A cewarta, wanann jakar da suke bayarwa akwai wani mai, mai santsi da idan mace ta ji wannan gullutu za ta dinga shafawa kafin ta je asibiti domin fara magance sankarar.

Jami’ar jinyar, ta yi amfani da wannan damar ta kirayi malaman addinai da sarakuna iyayen kasa da su dinga bai wa mazaje shawari na suna barin matan su suna zuwa awon ciki, domn samun kariya daga yawan zubar ciki da samun hanyar kariya daga kamuwa daga wannan cuta ta sankarar nono.

Daga karshe, ta ce kuma duk wani asibiti a jihar Jigawa yana kulawa da mata masu ciki wajen basu gidajen sauro kyauta da kuma bin duk wata hanya da za’a basu kulawar da ta dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *