Maniyyata 400 daga Sakkwato sun isa kasa mai tsarki

Maniyyata 400 daga Sakkwato sun isa kasa mai tsarki

Maniyyata 400 daga Sakkwato sun isa kasa mai tsarki

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

A ranar Lahadin da ta gabata jirgin farko ya kwashe maniyyata 420 da suka fito daga kananan hukumomin Gada da Wurno da kuma Yabo da ke cikin jihar Sakkwato zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ayyukan hajjin bana 2022.

A daren Lahadi da ake sa ran cewa, za a kammala kwashe maniyyatan jihar nan da ranar 27 ga watan Yuni 2022. A yayin da yake jawabi ga maniyyatan a babban filin jiragen sama na kasa da kasa da ke Sakkwato gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci maniyyatan da su kasance jakadu nagari a yayin da suke gudanar da ayyukansu na Hajji tare da bin dokokin kasar da hukumar Saudiyya ta shimfida.

Hakazalika, gwamna Tambuwal ya kuma jawo hankalin maniyyatan da su yi wa kasa da kuma jihar Sakkwato addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ganin yadda rashin tsaro ya yi wa kasar katutu. Daga nan sai Tambuwal ya jinjina wa kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ganin yadda aka cim ma dukkan nasarorin shirye-shiryen da aka gudanar a nan gida da kuma kasa mai tsarki.

Shi kuwa da yake tofa albarkacin bakinsa, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III ya shawarci maniyyatan da su tabbatar suna cin abinci a kai a kai da kada a yi wasa da yunwa a lokacin da ake gudanar da aikin ibada.

Daga nan Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi wa maàniyyatan fatan alheri kazalika da rokon kasar Saudiyya na ta sassauta dokar haramtawa masu shekaru 65 zuwa kasa mai tsarki, domin a taimaka ga wadanda ba su sami damar sauke farali ba.

Ya kuma tunatar da maniyyatan da su ci gaba da yin addu’o’i ga kasa da kuma jihar Samkwato a lokacin gudanar da ibada domin samun shugaba nagari wanda zai samar da ci gaban kasar nan da jihar Sakkwato.

Da yake jawabi a wajen bikin ban-kwana da maniyyatan, shugaban hukumar jin dadin alhazai na jihar, Alhaji Muntari Bello Mai Gona ya tabbatar cewa, hukumarsa ta kammala dukkan shiye-shiryen da ya dace a tsakanin Madina da kasar Makka domin jin dadin maniyyata a yayin da suke kasa mai tsarki.à

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *