Manoma, kada a raina ruwan shuka -Lawal Aliyu

Manoma, kada a raina ruwan shuka

Manoma, kada a raina ruwan shuka

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Lawal Idris

A makon da ya gabata, sarkin noma na jihar Kano, Alhaji Lawal Aliyu, ya yi kira ga manoma, tare da ba su shawara cewa, duk lokacin da damina ta kama, kada manoma su raina ruwan da ya sauka, duk rashin yawansa, kuma kada su raina hanyar gudanar da nomansu, domin a cewarsa, ita ce kadai hanyar da za ta kawo kowane irin ci gaba a kasar nan, a halin yanzu.

Sarkin noman, ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake ganawa da wakilin jaridar Albishir, inda ya bukaci matasa su rungumi harkar noma gadan-gadan, domin ita ce sana’a ga su matasan, sannan ya gargade su da su guji hanyoyin aikata daba, da shaye-shaye miyagun kwayoyi, domin su ne manyan gobe.

Alhaji Lawan Aliyu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta jiha, su ribanya kokarin da suke yi wajen tallafa wa manoma, domin a cewarsa, noma ba ya yiwuwa sai da tallafi, inda ya ja hankalin hukumomi su kara tallafa wa manoma a ko da yaushe.

Haka kuma ya yi fatan alkhairi ga gwamna Ganduje, da masarautar Kano, musamman Mai marbata San-Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, domin irin kokarin da yake yi wajen bunkasa karatun Alkur’ani maigirma, a ko da yaushe, a jihar Kano, wanda hakan shi ne babban abin da ya kawo zaman lafiya a jihar.

Daga bisani, ya ja hankalin al’umma das u yi kokari wajen wayar da kan al’umma su mallaki katin zabe domin samun shugabanni nagari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *