Manufofinmu, taimaka wa jama’ar Kano -MG Ibrahim Sani

Daga Rabi’u Sanusi Kano
Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar APM mai alamar rogo, MG Ibrahim Sani, ya bayyana abubuwa da yawa da suka kudurta wajen ganin jama’a a jihar Kano sun sami kyakkyawan canji cikin yardar Allah idan ya sami nasarar zama gwamnan Kano a zabe mai zuwa.
Ibrahim Sani ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da manema labarai jim kadan bayan kammala shiri kan manufarsa ga al’ummar jihar a gidan rediyon Pyramid na jihar Kano a ranar Larabar da ta gabata.
Ya ce, daya daga cikin manufarsa ta kawo canji ya sa duk inda suka je kamfen a halin yanzu sukan bayar da tallafin magunguna a asibitocin karkara da sauran yankunan Kano hadi da kayan haihuwa ga mata da rage masu tsaurin rayuwa.
Bayan tallafin magunguna, akwai batun samar da aikin yi ga matasa da wadanda suka kammala karatu da ma masu bukatar kasuwanci, akwai tsari mai kyau.
“Su kuma bangaren mata, akwai niyyar bude sashen koyar da sana’a domin magance matsalolin tallace-tallace da ke barazana ga yara mata wajen neman ilimi da ma abin da zai taimaka masu su sami kayan daki yayin hidimar aurensu a dukkan mazabu tare da bude masana’antu domin dogaro da kai.”
MG Ibrahim Sani ya kara da cewa, batun noma da kiwo kuwa, yana da shirin bunkasa noma ta hanyar gyaran dama-damai a jihar Kano ke da su da zai kara taimakawa wajen inganta noman rani da damina domin samar da kananan masana’antu.
Sannan ya yi alkawarin sanya hadimansa wajen gano irin bishiyoyin da suke iya amfanar da al’umma wajen bunkasa tattalin arziki, kamar kwara da kwalba-da-nono da zobo da ridi da sauransu domin samun kudin shiga.
A batun tsaro kuwa, ya bayar da tabbacin samar da ingantaccen tsaro, kasancewarsa tsohon jami’in tsaro kuma wanda ya jagoranci ayyukan tsaro aka sami nasarori da dama zai kawo ci gaba.
“Tuntuni na taba tattara tsofafin jami’an tsaro da ke jihar Kano domin tattauna yadda za a taimaka wajen samar da karin zaman lafiya a jihar Kano, inda kuma muke shirin bayar da kyakkyawan horo ga jami’an sintiri na Bijilanti wajen kara taimaka wa ma’aikatan tsaro, domin samun zaman lafiya a jiharmu ta Kano.”
Daga karshe ya ce, zai samar da cibiyar tattara bayanan sirri, wadda da an yi maganar matsala za su iya tura sako wajen da ya kamata a dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.