Masu ruwa-da-tsaki na APC: Sun bai wa Gawuna takara

Masu ruwa-da-tsaki na APC: Sun bai wa Gawuna takara

Ganduje yayin mika fom din takara ga Gawuna da Garo

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

A hukumance, gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da takarar mataimakinsa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna da ya yi takarar gwamnan jihar, a yayin da Alhaji Murtala Sule Garo zai take masa baya a matsayin mataimakin gwamna.

Wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Malam Abba Anwar, ta yi nuni da cewa, hakan ya biyo bayan taron masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar, da aka gudanar a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnati.

Ya bayar da tabbacin cewa, taron ya amince bai-daya da batun takarar Gawuna da Garo, domin kuwa sai da aka cika kowane sharadin da jam’iyyar ta gindaya kafin a kai ga zartar da kudirin taron.

Da yake magana kan cancantar Gawuna, gwamna Ganduje ya ce, “Mutum ne mai mutunci da kamala wanda ya san abin da yake daidai da abin da ba daidai ba, kuma abin dogaro mai biyayya” Ya ce, “A matsayin Gawuna na mataimakin gwamna, ya yi amfani da ofishinsa wajen kasancewa mataimaki mai biyayya kuma abin dogaro”.

Da ya juya kan Murtala Sule Garo, gwamnan ya ce, “Hakika kwamandan yaki ne, mai biyayya da zage damtse kuma marar tsoro, domin idan ka sami mayakin dan siyasa mai yaki kai-tsaye babu indainda, ka sami mai kuzari, mai biyayya wanda ba shi da tsoro, to wannan shi ne Murtala Sule Garo”.

Har ila yau, a wajen taron, ‘yan majalisar tarayya masu wakiltar jihar Kano wadanda suka halarci taron, ta hannun shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya bayar da sanarwar amincewarsu ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ya yi takarar majalisar dattijai daga shiyyar Kano ta Arewa, mai kananan hukumomi 13, ta hanyar mika masa fom Shi kuwa shugaban majalisar dokokin jihar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya yi alkawarin taya gwamnan yakin neman zabe babu kakkautawa.`

A nasa bangaren, shugaban dattijan jam’iyya, Alhaji Nasiru Aliko Koki, ya bayyana cewa, su suka bai wa gwamnan shawara kan halin da siyasar jihar ke ciki, kuma hakan shi ne mafita a shekara ta 2023 matsawar APC na son ta kai bantenta.

Daga nan gwamnan ya yaba wa ilahirin wadanda suka halarci taron da kuma amincewa da shawara da kudirin da aka zartar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *