Masu sace ‘yan-makaranta za su kashe ililmi a Arewa –Buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya umarci sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an leken asiri da su tabbatar da an sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su kuma cikin aminci.
Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga shugaban, Garba Shehu ya fitar ya ce, Buhari ya nuna damuwa game da karuwar hare-hare a Kaduna da Neja musamman kan daliban makarantu.
Shugaban wanda ya ba da umarnin kara girke dakarun tsaro a yankunan da suke kara zama hadari, ya shawarci jami’an da su yi aiki da hankali da dabara wajen tabbaar da an sako daliban da aka sace cikin aminci.
Buhari ya ce, yawan sace daliban da ake yi a makarantu musamman a jihohin Arewacin Nijeriya zai haifar da wani gagagrumin koma baya ga harkokin ilimi, da kuma yadda iyaye za su rika kai yaransu makarantu.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su bayar da hadin kai ga shirin Majalisar Dinkin Duniya na tabbatar da aminci ga makarantu, wanda gwamnatin tarayya da runguma