Masu sana’ar magungunan Musulunci, nafdac sun shirya bita Saboda nagartar magani

nafdac sun shirya bita ga masu sanao'in gargajiya

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kungiyar masu sana’ar magungunan Musulunci, reshen jihar Kano da hadin gwiwar hukumar NAFDAC sun gudanar da taron bita na yini a kan nagartar magungunan.

Taron ya gudana a dakin taro na Mambayya, da ke unguwar Gwammaja cikin birnin Kano, a ranar Laraba da ta gabata, ya sami halartar masu sana’ar sayar da mugungunan Musulunci daga kananan hukumomi 44 na jihar. Da yake jawabi a taron shugaban kungiyar, Alhaji Nasiru Muhammad Nasir Albariyya ya ce, taron na hadin gwiwa ne da NAFDAC domin fahimtar juna domin a gudu tare a tsira tare.

Ya yi nuni da cewa, a cikinsu akwai masu magunguna na Musulunci da na gargajiya da suke sarrafa su a inganta su a sanya a kwali da kwalabe domin haka suna da alaka da kulawar NAFDAC. Kuma ya ce, hukumar NAFDAC na kokari wajen ganin suna inganta sana’ar su.

Alhaji Nasir Muhammad Nasir ya ce, yan kungiyar suna tafiyar da tsaretsaren hukumomi masu ruwa-da-tsaki da kula da sana’ar. A kungiyar akwai dimbin masu harkar gudanar da magunguna da suka hada da magidanta da matasa da ma mata na aure a gidaje da zawarawa.

A yayin taron an gabatar da makaloli guda biyu da aka yi bayani a kan magungunan Musulunci wanda Malam Ibrahim Mansur Gadar Salga ya gabatar da kuma makala mai taken; hanyoyi da dabaru na inganta magani daga Dokta Abdurrahman Minas. Cikin jami’an hukumar NAFDAC da suka halarci bitar Malam Idris Gimba ya nuna jin dadinsa bisa yanda masu magunguna suka game abin da hukumar ke yi mai muhimmanci.

Sannan ya yi bayani kan tsare-tsaren yanda za a yi alaka domin yin magani mai inganci a dokokin hukumar.

Shi ma jami’in hukumar Mustapha Adamu ya yi bayani kan matakai da ake bi wajen hanyoyi domin inganta magani. Kungiyar masu magungunan Musulunci ta mika takardun girmamawa ga shugaban hukumar NAFDAC na Kano, Alhaji Shaba Muhammad da mai taimaka wa gwamna Ganduje a kan magungunan gargajiya, Alhaji Muhammad Khamis Kibiya da kuma uban kungiyar Alhaji Auwal Bature Abubakar.

Cikin wadanda suka halarci taron akwai shugabanin kungiyar reshen kasuwanin Sabon Gari da na Kurmi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *