Masu sana’oi, a rinka kwatanta gaskiya da amana -Gemu mai nama

Daga Wakilinmu
An yi kira ga masu sana’oin hannu daban daban dake jihar Kano da kasa baki daya cewa, su rika kwatanta gaskiya da amana tare da sanya tsoron Allah a duk lokacin da suke gudanar da sana’arsu, ko sa samu tsira a wurin Allah.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin sakataren sayar da nama, Alhaji Umar Gemu mai Nama da ke kan hanyar zuwa asibitin Nassarawa a Kano, Alhaji Ibrahim Lausu, a lokacin da yake zantawa da jaridarAlbishir kwanakin baya a Kano.
Ibrahim Lausu ya kara da cewa, duk wanda ya tsare gaskiya da amana idan Allah ya so zai samu daukaka da ci gaba a cikin sana’arsa. Alahji Ibrahim Lausu da ya fito daga garin na Lausu da ke cikin karamar hukumar Rano, ya shawarci matasan da suka fito daga yankunan karkara da birane cewa, lallai lokaci ya yi da su nemi sana’oin dogaro da kai mai makon su jira sai gwamanti ta samar masu aiki, idan suka kware a kan sana’ar da suka koya za su iya koyawa wadansu.
Sai ya yi amfani da wannan dama da kira ga gwamnatin Nijeriya cewa, ta kula sosai a kan rayuwar matasan kasar nan musamman samar masu da wuraen sana’oin dogaro da kai, domin yawancin abin da ke faruwa na aikata abu marasa kyau da matasan ke yi rashin aikin yin a daya daga cikin abin dake haifar das u .
Ya kuma jawo hankulan iyaye cewa, lallai su kara sanya idanu sosai akan tarbiyar yayan su , saboda wasu lokuta iyaye na sako sako akan kula tare da sanya idanu akan yaran su.
Daga karshe, ya yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen rashin tsaron da ke addabar kasar nan musamman akan hanyoyi da ake yawan garkuwar da mutane a halin yansu.