Mata manoma suna samun goyon baya a gwamnatin Jigawa -In ji Hajiya Salamatu

Daga Jabiru Hassan, Dutse
Shugabar kungiyar mata manoman shinkafa ta ganu war kuka watau ‘Ganuwar Kuka Women Rice Farmers’s Association’ da ke yankin karamar hukumar Auyo Hajiya Salamatu Ahmed Ganuwar Kuka, ta ce gwamnatin jihar Jigawa ta na bai wa mata manoma goyon bayada kuma karfin gwiwar yin noma domin wadata kasa da abinci.
Tayi tsokacin cikin zantawar su da Albishir a birnin Dutse, inda ta bayyana cewa, ba domin samun matsalar ambaliyar ruwa a wadansu sassa na jihar ba, da ko shakka babu mata manoma sun bayar da mamaki na shinkafar da suka shuka, a damunar bana, sannan aikin da suka yi ya yi nuni da cewa, mata a jihar ba a barsu a baya ba wajen amsa kiran gwamnatin Tarayya na wadata kasa da abinci.
Hajiya Salamatu Ahmed ta ce zan yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga gwamnatin Muhammadu Badaru Abubakar bisa kokarin da yake yi wajen bunkasa noma a jihar, tare da bai wa mata manoma kwarin gwiwar yin noma da kiwo kamar yadda ake gani a fadin jihar rani da damuna.
In ji ta. Hajiya Salamatu, wadda ita ce shugabar mata ta kungiyar manoma shinkafa ta kasa reshen jihar ta Jigawa watau “RIFAN” ta godewa ma’aikatar gona ta jihar da hukumar bunkasa aikin gona ta jihar da hukumomin da ke da ruwada-tsaki ta fannin noma na ciki da wajen kasarnan saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen ganin jihar ta zamo abar misali ta fuskar noma a kasar.
A karshe, shugabar mata manoman ta yi fatan cewa, gwamnatin jihar da hukumar bayar da agaji ta kasa da su hada karfi wajen ganin an tallafa wa manoman da suka yi asarar kayan amfanin gonar su ta sanadiyyar ambaliyar ruwa da aka samu a bana, tare da yin kira ga manoma da kada wannan lamari ya karya masu kwarin gwiwar ci gaba da noman da suka yi.