Matasa, a bayar da hadin kai wajen yin zabe -Umaru Gemu

Daga Shafiu Yahaya
An nemi daukacin ‘yan Nijeriya, musaman matasa maza da mata a Nijeriya, kuma suka fi zuwa kada kuria a rumfunan zabe, da su tabbatar sun bayar da hadin kai wajen yin zabe lafiya.
Kiran ya fito daga bakin Alhaji Umaru Gemo mai gasa naman rago, a lokacin da yake nasiha kan zabe ta bakin sakataransa, Mallam Ibrahim Lausu Rano.
Ya ce, mutanen Nijeriya, masu san zaman lafiya, sun fi masu san tayar da hankali yawa, don haka, wannan abin godiyar Allah ne, kuma Kano Allah ya albarkace ta da malamai da ‘yan kasuwa da sarakuna da sauran al
umma masu dimbin baiwa kuma ana ta addu’a wanda wannan na taimaka wa Kano wajen zaman lafiya.
Ya kuma yaba bisa kokarin gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, kan ci gaban Kano to kowace fuska. A karshe, ya yi kira ga masu hali da hukumomi, su taimaka wa talakawa masu karamin karfi, musamman a wannan lokaci na canjin kudi da karancin kudi.
Ya kuma yi fatan samun shugabanni nagari a zaben gaba, inda kuma ya nemi daukacin shugabanin Nijeriya, da su yi adalci da amana da rokon gaskiya da tsoran Allah domin ci gaban jihar Kano da Nijeriya, baki daya
.