Matasa, a guje wa shiga bangar siyasa -Sharif Sidi

Shariff Auwal Siddi
Danjuma Labiru, Daga Gombe
Yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara karatowa, shugaban majalisar mawakan kasidun Hausa ta Nijeriya watau, Ushakun Nabiyyi Rasulil A’azam, Shariff Auwal Siddi Bolari, ya yi kira ga matasa a Jihar Gombe da Nijeriya su guji duk wani abu da zai iya kawo tsaiko ga zaman lafiya da tsaro a jihar da kasa baki daya.
Shariff Auwal Siddi Bolari, ya yi wannan kiran jim kadan bayan kammala taron shekara-shekara na majalisar a Gombe. Ya ce, dole ne iyaye su sanya ido sosai kan ‘ya’yansu, su kare su daga shiga hatsaniyar siyasa, yana mai jaddada cewa, majalisar ta umarci mambobinta a fadin kasa da su rika rubuta kasidu da za su karfafa zaman lafiya da hadin kan al’umma.
Ya kuma bukaci ‘yan siyasar da su rika tallafa wa matasan a hanyar neman ilimi da ba su tallafin sana’o’i domin dogaro da kai.
Ya sake yin kira ga matasa su tabbatar sun mallaki katin zabensu na dindindin, watau (PBC), domin zaben ‘yan takarar da suke so a shekarar 2023.
Bolari ya kara da cewa, shirye-shiryen majalisar sun yi nisa na bikin sabuwar shekarar Musulunci mai zuwa, inda za a gudanar da abubuwa daban-daban, ta yadda bikin zai fi na baya armashi da kayatarwa.
A nasa bangaren, uba a majalisar, Ahmad Musa Muhammad Sahibul Khairati, ya yaba wa malaman addinin Musulunci bisa yadda suka gudanar da tafsiran Kur’ani mai girma a watan Ramadan da ya kare, dama irin addu’o’in da suka yi na neman zaman lafiya da tsaro ga kasa baki daya.
Sahibul Khairati ya yi kira ga malamai da sauran al’umma su kara zage damtse wajen addu’ar Allah ya zaba mana ‘yan takara mafiya alkhairi a mukamai daban-daban a zaben 2023.