Matasa, a kama sana’ar noma -In ji Ali Branco

Matasa, a kama sana’ar noma -In ji Ali Branco

Ali Branco

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

 An yi kira ga matasan jihr Kano da su kama sana’ar noman rani da damina domin ci gaba da kasancewa cikin zamantakewa mai albarka da kuma amsa kiran gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.

Kiran ya fito ne daga Ali Adamu Kunnawa wanda aka fi sani da Ali Branco da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a yayin da wakilinmu ya ziyarci katafariyar gonar da yake noman rani, inda ya bayyana cewa, matasa su ne ginshiki ci gaban kowace kasa, domin haka yana da kyau su kasance masu abin yi ta yadda za su dogara da kansu.

 Ya ce, sana’ar noma tana da albarka sannan akwai samar da ayyukan yi da kawar da hankalin mutane daga tafiya birane neman ayyukan yi daga yankunan karkara, domin haka yana da kyau kowa ya tashi tsaye neman arziki da dogaro da kai ta yadda zamantakewa za ta ci gaba da yin kyau.

Malam Ali Adamu Branco ya bayyana cewa, yana noma masara da gero da maiwa da wake da dawa da kuma gyada idan damina ta sauka, sannan yana noma albasa da tumatur da alayyahu da tattasai da sauran kayan lambu da rani domin ganin ya kasance cikin dogaro da kai saboda ganin yadda zamani ya juya.

 Matashin manomin ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kulawa da matasa da take yi wanda a cewarsa, hakan yana taimaka wa wajen rage marasa aikin yi da kawar da aikata laifuffuka cikin al’umma, sannan ya roki gwamnati da ta samar da tallafi ga matasa manoma ta yadda za su rubanya ayyukansu na noma rani da damina.

 A karshe, Ali Adamu Branco ya yi kira ga shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa da ta gyara masu Dam din Kunnawa wanda kafin karyewarsa yana samar da damar yin noman rani ga dimbin al’umma inda ake noma kayan lambu na miliyoyin kudade, tare da fatan cewa, wannan sabuwar shekara ta zamo mai tarin albarka ga al’ummar jihar Kano da kuma kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *