Matasa, a kama sana’o‘in dogaro da kai -Makaman Panshekara

Alhaji Gambo Abdu

Alhaji Gambo Abdu

Tura wannan Sakon

Labarai Daga Ahmad S. Ahmad

A cikin makon da muke ciki ne Makaman Panshekara, Alhaji Gambo Abdu Kayi ya buqaci matasa kan su zage damtse wajen koyon sana’a, domin su samu damar dogaro da kansu tare da kaucewa zaman kashe wando cikin mutane.

Makaman Panshekara ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a masarautar, a’inda ya qara da cewa, ya kamata ka da matasan su rinqa raina sana’a, domin kowacce iri ce in dai an rinqi gaskiya za ta iya zama sababin arzikin mutum.

Da ya koma ta kan masarautar Panshekara kuwa ya jaddada qudirinsa na ganin an samu bunqasar masarautar, wanda ya nemi duka wanda ke da wani abu da ya shige masa gaba ya gabatar masu domin daukar matakin da ya dace

Haka kuma ya qara miqa godiyarsa ga hakimin Kumbotso, Alhaji Ahmad Ado Bayero da Dagaci, Alhaji Ibrahim Lawan kana amincewar da suka yi aka ba su muqamai a masarautar.

Daga Karshe, ya nemi hadin kan jama’a domin ci gaba da yi masu addu’o’in fatan Alheri, ta yadda za su samu samar da walwala ga mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *