Matasa a kama sana’o’in dogaro da kai -Shugaban UNICARE

Queues at ATM - 1

Tura wannan Sakon

Daga Shafiu Yahya

Daya daga cikin malaman jami`a, kuma likita, Dokta Aminu Idi, ya ce, rayuwar na bukatar aiki da kwazo da tanadi da tattali da nuna basira da kuma yin tinani a matsayinka na dan’adam, ta hanyar yin da dogaro da Allah, musammam ta hanyar sama wa kanka sabon aiki a matsayinka na ma`aikaci ya zama wajibi ka samawa kanka sana`a bayan aiki ta yadda ko da ka yi ritiya daga aiki ba wata matsala.

Ya ce, akwai sana`ar noma ko kiwo a matakin farko har ka samu zama babban manoni wanda zai iya ciyar da kansa a shekara har ma ka taimaka wa unguwarku karamar hukuma ko jihar ku da kasar ku baki daya.

Wannan zai taimaka maka wajen tsayuwa a kan gaskiya ta aiki ba tare da wani kokari na aikata rashin gaskiya ba.

Har ila yau, Dakta Aminu Idi, ya ce, shugabanni suna bukatar shawarwari daga al`uma amma ba kalubalantarsu domin cewa, a ko’ina ka ga abu da ba dai dai ba wajibi ne ka yi gyara koda hanunka ko da bakinka idan kuma ka yi shiru to babu haka ake so ba an fi son gyara a dukkan wani lamari kuma wajibi ne shugabani su zama masu adalci da kishin kasa da al`umarsu, domin kowa zai yi bayani a kan abin da ya aikata a duniya da kuma gobe kiyama, kuma kuskure ne mutum ya rika zagin kasarsa ko shugabaninsa ko kuma mutum ya rika aibata al`umma da yake cikinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *