Matasa, a nemi ilimi – In ji Abubakar

Abubakar Gali
Daga Musa Diso
Daya daga cikin yaran da suka sauke Alkur’ani a makarantar Sinhaji Islamiyya da ke Lokon makera a karamar hukumar Gwale, Alhaji Abubakar Gali Abdullahi dan Birniwa ya shawarci yara da su ci gaba da neman ilimin addini da na zamani domin samun rayuwa mai kyau.
Ya yi tsokacin ne a tattanawa da wakilinmu jim kadan bayan kammala bikinsaukar karatun karo na 3 a makarantar. Ya ce, yana da kyau yara su sami ilimi na Addini da kuma na zamani domin gudanar da rayuwa mai albarka sannan ya jaddada cewa, ilimi shi ne gishirin zaman duniya.
Malam Abubakar Gali Abdullahi dan Birniwa ya bukaci iyayen yara da su kara kokari wajen bai wa ‘ya’yansu kwarin gwiwa samun ilimi tun daga tushe.
Daga karshe, Abubakar ya yi godiya ga shugaban makarantar da malaman saboda juriya da hakuri da suka yi wajen koyar da karatu a w makarantar Sinhaji Islamiyya, inda kuma ya ja hankalin dalibai da suke karatu a makarantar da su kara jajircewa wajen neman ilimi