Matsalarmu, rashin wadatatun kayan aiki a asibitoci -Banef Ephraim

Banef Ephraim
Labarai daga Abdullahi Sani Doguwa
An yi kira ga gwmnati da ta tallafa wa kananan asibitoci da ke yankunan karkara da suke karbar lururori iri iri dabandaban kuma suke da karancin kayan aiki.
Bayanin haka ya fito daga bakin Mista banef Ephraim, shugaban asibitin lura da iyaye mata masu dauke da juna biyu, da karbar masu da larurori iri daban-daban watau (MARTERNITY HOSPITAL) hayin gada, da ke Samunaka a yankin karamar hukumar Lere, jihar Kaduna.
Ya ce, tun da farko ya fara da bayyana irin na mijin kokarin da asibitin yake yi a koda yaushe ta fuskoki daban-daban da ya hada da duba lafi
yar mata masu nakuda da kuma yin awo da lafiyar yaransu, idan kuma hakan ta faskara sukan tura ne babban asibiti cikin gaggwa.
Mista Banef Ephraim, ya ce, ban da duba lafiyar iyaye mata da yaransu, asibitin na karbar emergency, watau jinyar gaggawa, a koda yaushe, sai dai babbar matsalar da suke fuskanta ita ce, rashin wadatatun kayan aiki, watau na’urori da sauransu.
Banef ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga hukumomi da gwamnati da su taimaka su duba halin da asibitin ke ciki wajen samar masu da kayyaki.
Mista Banef Ephraim ya kara da cewa, yau shekaru 12 da bude wa ya fara aiki da ma’aikata akalla 12 ciki har da masu gwaji, wadanda sun shahara kan bangarori dabandaban a asibitin da kuma masu karbar haihuwa, da wadanda ake ce Community prasturacture, masu zuwa yankunan karkara, domin duba majinyata.