Matsalolin tsaro a Nijeriya: Taron tunawa da Malam Aminu ya gano bakin zaren

Bashir Magashi
…bayanin sirri, domin yin haka
An lura da cewa,sanya rahotanni kan bincike cikin kwandon shara shi ke mayar da hannun agogo baya wajen sha’anin tsaro da siyasa a Nijeriya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron tunawa da gwarzon dan-kishin kasa, Malam Aminu Kano,a babban dakin taro na cibiyar Dimukuradiyya ta Mambayya,Gwammaja, Kano,tsohon babban kwamandan runduna ta 3 ta sijojin Nijeriya da ke Jos, Manjo-janar Saleh Maina,mai ritaya,ya yi bayani daki-daki kan yadda kwamitin shirye-shiryen mika mulki a shekara ta 2015 ya tsara rahoto kan tsaro da sauran al’amura ya mika wa gwamnati,amma shiru kake ji.
Ya ce, da yake yin sharhi kan jawabin da babban mai jawabi a wajen taron, Janar Martins Luther Agwai ya gabatar, Janar Maina ya ce,babu abin da zai magance matsalar tsaro kamar musayar bayanan sirri a-kai-a-kai amma ba adana bayanan sirri ba,domin yin babu wata fa’idar a-zo-a-gani.
Janar Saleh ya bayar da misali da harin da aka kai wa Amirka mai taken Sept.11,inda ya ce,ka ga a nan adana bayanin sirri ba ta yi rana ba.
Ministan tsaro,Janar Bashir Magashi ya sami wakilcin Manjo-janar Ahmad Tijjani Adamu, shugaban taro,Farfesa Abddullahi Mahdi ya sami wakilcin Farfesa Muhammad Mainoma, sai mai sharhi na biyu Farfesa Dung Pan Sha, daga cibiyar hazarin muhimman bukatun kasa(NIPSS) da ke Kauru kusa da Jos,duk sun yi na’am da jawabin Janar Agwai cewa,harkar tsaro ta kowa da kowa ce, sojoji wani bangare ne na masu-ruwa-da-tsaki, saboda haka,a hada hannu a yi aiki tare domin dorewar Dimukuradiyya a Nijeriya.