Matsalolin tsaro a Nijeriya:

Matsalolin tsaro a Nijeriya:
Taron tunawa da Malam Aminu ya gano bakin zaren
An lura da cewa, sanya rahotanni kan bincike cikin kwandon shara shi ke mayar da hannun agogo baya wajen sha’anin tsaro da siyasa a Nijeriya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron tunawa da gwarzon xan-kishin qasa, Malam Aminu Kano, karo na 19 da kuma cikar Malam Aminu Kano shekaru 38 da rasuwa, a babban xakin taro na cibiyar Dimukuraxiyya ta Mambayya, Gwammaja, Kano, tsohon babban kwamandan runduna ta 3 ta sojojin Nijeriya da ke Jos, Manjo-janar Saleh Maina,mai ritaya, ya yi bayani daki-daki kan yadda kwamitin shirye-shiryen miqa mulki a shekara ta 2015 ya tsara rahoto kan tsaro da sauran al’amura ya miqa wa gwamnati, amma shiru kake ji. Ya ce, da yake yin sharhi kan jawabin da babban mai jawabi a wajen taron, Janar Martins Luther Agwai ya gabatar, Janar Maina ya ce, babu abin da zai magance matsalar tsaro kamar musayar bayanan sirri a-kai-a-kai amma ba adana bayanan sirrin ba, domin yin haka babu wata fa’idar a-zo-a-gani. Janar Saleh ya bayar da misali da harin da aka kai wa Amirka mai taken Sept. 11, inda ya ce, ka ga a nan adana bayanan sirri ba ta yi rana ba. Ministan tsaro, Janar Bashir Magashi ya sami wakilcin Manjo-janar Ahmad Tijjani Jibrin, shugaban taro, Farfesa Abddullahi Mahdi ya sami wakilcin Farfesa Muhammad Mainoma, sai mai sharhi na biyu Farfesa Dung Pam Sha, daga cibiyar nazarin muhimman buqatun qasa (NIPSS) da ke Kuru kusa da Jos,duk sun yi na’am da jawabin Janar Agwai cewa, harkar tsaro ta kowa da kowa ce, sojoji wani vangare ne na masu-ruwa-da-tsaki, saboda haka, a hada hannu a yi aiki tare domin xorewar Dimukuraxiyya a Nijeriya. Shugaban majalisar Malaman Nijeriya, Sheikh Ibrahim Khalil yana daga cikin hamshaqan mutanen da suka halarci taron kuma shi ya rufe taron da addu’a.
Shugaban jami’ar Bayero Farfesa Sagir Adam Abbas shi ne babban mai masauki.