Matsawar na zama shugabar APC, zan kare yanci Mata -Fatima Jajere

Fatima Jajere

Tura wannan Sakon

Daga Danjuma Labiru Bolari  Gombe

A kokarin ta na kwato wa mata ‘yanci a Arewa maso gabas, Hajiya Fatima Isa Jajere, ta fito neman shugabancin mata na Arewa maso gabas na jam’iyyar APC inda ta yi alkawarin ganin ta tsaya masu domin a dama da su a harkokin siyasa.

Fatima Jajere,  gogaggiyar ‘yar siyasa ce da ta jima tana bayar da gudumawa wajen ganin ta hada kan mata wanda tun kafin ta fara siyasa take taimaka wa matan yankin, wajen koya masu sana’o’in hannu, sannan take tallafa wa masu kananan jari a karkashin kungiyarta mai suna F-Jajere Foundation.

 Ta ce, siyasa dole ne sai da mata domin mace ce tasan ciwon ‘yar uwanta mace kuma ganin ba a damu da taimaka masu a siyasan ce ba, yasa ita da take ciki ake damawa da ita take neman shugabar mata na Arewa maso gabas domin ganin cewa, an dama da su.

A zantawar ta da manema labarai, Fatima Isa  ta ce, a wannan lokacin ne ya dace a shigar da mata a tafiyar da ake yi domin an bar su a baya kuma batun gaskiya kamata ya yi a ce suna sahun gaba saboda sune masu zabe da suke da kuri’u a hannu.

 A cewar ta ta fito takarar ne domin wakiltar matan yankin, domin ganin cewa, mata sun rasa jagoranci bayan su suke yawo a rana da dare wajen ganin sun zabi shugabanin da suke ganin za su shugabance su sai ga shi ana yi babu su.

Hajiya Fatima Jajere ta ce, ko a zaben da ya gabata na 2019 mata sun bayar da kuri’u da yawa amma sai ga shi ba su da wakilci a ma’aikatun gwamnati yadda ake bukata.

Ta yi amfani da wannan damar ta yi wa mata Albishir da cewa, muddin ta zama shugabar mata ta yankin, mata za su san sun samu wakilci kuma za ta yi siyasa kofa a bude wajen bai wa kowacce mace dama domin ta kawo korafin ta a share mata hawaye.

Hajiya Fatima Jajere ta kirayi shugabani da cewa, yana da kyau ana tallafa wa mata a dinga tafiya da su a duk wata tafiya ta siyasa, domin karfafa masu guiwar fitowa siyasa.

Ta ce, a Arewa maso gabas mata an bar su a baya domin idan mace ta fito siyasa sai kaga ba a karfafa mata gwiwa da zarar an kafa gwamnati kuma sai a yi babu su inda ta ce, tana so ta canja tsari ya zama komai ana yi da mata. Daga karshe, ta yi kira ga mazaje da su dinga barin matansu suna fitowa ana damawa da su a siyasa suna ci gaba da bayar da ta su gudumawa, kuma a daina yi masu mummunan fassara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *