Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani RA: Sha’irai sun jinjina wa Dankwambo

Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani RA: Sha’irai sun jinjina wa Dankwambo

Maulidin Shehu Ahmadu Tijjani RA:

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari, daga Gombe

Shugaban kungiyar mawakan Annabi na kasa, Ushakun Nabiyi Rasulil A’azam, Sharu Auwal Siddi Bolari, Talban Sharifan Nijeriya ya jinjina wa tsohon gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo kan yadda a baya ya hidimta wa mabiya darikar Tijjaniya wajen daukar nauyin maulidi.

Sharu Auwal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan shirye-shiryen maulidin sheikh AhamaduTijjani Abul Abbas, na wannan shekarar da za’ayi a ranar 24 ga Satumba, 2022 a Gombe. ce, Tsohon gwamnan shugaba ne da a lokacin mulkinsa ya dauki dawainiya ‘yan darika zuwa kasar Senegal domin halartar maulidin shiekh Ahmadu Tijjani, har ya gama mulki wanda a yanzu sun rasa irin wannan damar kuma ga shi duk ‘yan kungiyar Ushakun Nabiyi idan suka shigo daga ko’ina su ne masu masaukinsu.

Auwal Siddi, ya kara da cewa, ana kan shiryeshiryen maulidin shiekh Ahmadu Tijjani, amma har yanzu babu wani tallafi sai dai su a matsayinsu na ‘yan kungiyar suna shiri kuma a lokacin taron suna shirye da su yi wa kasa addu’a na zaman lafiya da kuma fatan a yi zabe lafiya.

Ya ce, sha’irai masu begen Annabi mutanen kirki ne kar a dinga daukarsu ‘yan bambadancin siyasa domin a irin wakensu ba sa zambo kuma basa zagin kowa.

Talban Sharifan ya ja hankalin sha’irai sosai da cewa, ganin mafi yawansu matasa ne su zama masu sana’a kar su zama marasa aikin yi a rinjaye su da wani abu su shiga layin ‘yan ta’adda ko ‘yan bangar siyasa domin haka su kiyaye.

Ya yi amfani da damar ya yi kira ga shugabanni na sauran jihohi da su hada kai su nausa kungiyar su gaba. Daga karshe, ya ce, tun a baya kungiyar take kira da duk wani mamban ta ya mallaki katin zabe domin zabar shugaban da zai zama mai adalci, sannan kungiyar ta ci moriyarsa kamar yadda sauran kungiyoyi suke cin moriyar ribar mulkin siyasa kuma jama’ar jiha masu shaida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *