Mayar da Kano birni na zamani, inganta tsaro –KNUPDA

Tura wannan Sakon

Daga Rabi’a T Mai fata

Jihar Kano ta yi suna wajen kasuwanci a kasar nan, har ma da kasashen ketare. Jihar Kano ce kan gaba a fannin hada-hadar kasuwanci kuma cibiyar tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.

Bugu da kari, jihar Kano ita ce jihar da tafi kowacce jiha yawan jama’a a Nijeriya. Kididdiga ta nuna cewa, akalla akwai mutane miliyan 20 a cikin jihar ta Kano.

Kano tana karvar baki akalla mutane dubu biyar a kullum, cikinsu a kwai masu zuwa Kano cirani, sannan mafi yawa daga cikin irin wadannan baki suna zuwa Kano ne domin dalilin kasuwanci da makamancin hakan.

Wadannan dalilan ne ya sa gwamnatin jihar Kano ta fifita fannin tsaro a kan wasu ayyukanta na ci gaban al’umma, domin idan babu cikakkon tsaro duk wasu ayyukan ci gaba ba za su yiwu ba, idan babu cikakken tsaron rayuka da kadarorin jama’a. Bisa wannnan dalilin, gwamnatin jihar Kano ta mayar da hankalinta wajen samar da tsaro, shi yasa ake samun wanzuwar zaman lafiya tsakanin dubban jama’a da kuma kabilu mabambanta da ke zaune a jihar.

Hakan ya taimaka wajen kau da yanayi na tashin hankalin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karvar kudin fansa. Baya ga haka, gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana mutukar kokari wajan samar wa matasa ayyukan dogaro da kai.

Akalla, alkalma sun nuna cewa, gwamnatin Ganduje ta samar wa matasa fiye da miliyan daya ayyukan yi, sannan wasu matasan an koyar da su sana’o’i iri daban-daban. Amma abin mamaki shi ne, duk da irin wadannan ci gaban da aka samu da kokarin wanzar da zaman lafiya da gwamnatin jihar ke yi, akwai wata barazana da jama’ar Kano suke fuskanta. Wannan kalubalen kuwa shi ne, na varayi masu kwacen wayoyin sadarwar mutane a wurare daban-daban a cikin birnin Kano.

Kadan daga cikin unguwannin da ke fama da ta’asar kwacen waya sun hada da irinsu Dorayi da titin gidan gwamna da Kofar Mata da kuma wasu unguwannin da babu zirga-zirgar mutane sosai.

Haka zalika, abin bai tsaya a nan ba har cikin babur mai kafa uku watau A-daidaita-sahu kwacen suke yi. A kwananakin baya, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi holin wadanda ta kama su da laifuka kimanin mutane 1,220 wadanda take tuhumar su da laifuka daban-daban, amma mafiya yawa daga cikin su tana tuhumar su ne da laifuffukan da ke da alaka da kwacen wayoyin sadawar mutane. Wasu daga cikin varayin wayoyin ma sun aikata kisan kai kafin su kwace wayoyin wadanda suka kashe har lahira.

A birnin Kano, da yawa mutane sun san cewa, harabar filin wasan kofar Mata, watau Sani Abacha Stadium da kewayen ta ya yi fice wajen zama dandalin varayi masu kwacen wayoyin mutane, inda a wasu lokutan akan kashe mutum idan an sami jayayya a tsakaninsu.

Cikin irin kokarin da hukumomin jihar Kano ke yi wajen shawo kan badakalar kwacen wayoyin jama’a, hukumar tsarawa da raya birnin Kano, watau Kano State Urban Planning and Development Authority (KNUPDA) ta shige gaba wajen samar da hanyoyin dakile kalubalen kwacen wayoyin mutane ta hanyar wargaza duk wani dandali ko matattarar varayin wayoyin mutane.

Misali shi ne, bayan samun izini daga gwamnatin jihar Kano, Hukumar tsarawa da raya biranen jihar Kano, watau KNUPDA ta rurrusa duk wani kangon da ke kewaye da filin wasan na Sani Abacha da ke Kofar Mata, inda aka gano varayin wayoyi na taruwa don aikata ta’asarsu.

Bayan hukumar ta killace ta kuma tsabtace wuraren, sai ta dukufa wajen gine-ginen manya da kananan shaguna tare da hadin gwiwar wasu ‘yan kasuwa masu zuba jari domin ci gaban jihar Kano.

Yanzu huka an kewaye filin wasan da shaguna, wajen ya zama wata cibiyar kasuwanci a Kano maimakon akasin hakan a da, inda dandalin filin wasan da kewayensa ya kasance matattarar varayi da shaye-shaye da masu kisa da kuma kwacen wayoyin mubaya aka sami wata ‘yar hatsaniya.

Bayan haka, hukumar karkashin shugabancin Arc. Suleiman Ahmad Abdulwahab ta bude wata kafa a hedikwatarta domin sauraren korafe-korafen Yanzu dai za a iya cewa wadannan ayyukan da hukumar ta aiwatar ya taimaka mutuka wajen hana sace-sace da kwacen wayoyin sadarwar jama’a a wadannan wurare. Abin sha’awa hakan ya dada bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin jihar Kano baki daya.

Cikin irin kokarin da hukumar ke yi wajen inganta tsaretsaren birnin Kano domin shawo kan duk wata matsala da za ta iya kawo cikas wajen tsaretsare da gine-ginen cikin birnin Kano. Hukumar ta KNUPDA ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen mallakar na’ura mai tsarin jirgin sama watau (Drone) wanda ke iya hangen nesa da daukar hotunan cikin birnin Kano da kewaye domin bunkasa ayyukanta.

Wannan na’urar kimiyar zamani ta dada inganta ayyukan hukumar ta wajen gano gine-ginen da aka yi su ba tsari ko kawo barazana ga al’ummar cikin birnin Kano baki daya.

Har ila yau, hukumar tsarawa da raya biranen jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da irin wadannan ayyuka domin tsaron birnin Kano da cigabansa. Yanzu haka, hukumar ta gudanar da makamancin wannan aiki a wata makabarta da ke garin Kano, inda kwanakin da suka shafi tsare-tsaren ginegine a cikin birnin Kano da kewayensa.

Sannan kuma shi ma Masallacin idi da ke Kofar Mata, hukumar Tsarawa da raya biranen jihar Kano (KNUPDA) ta aiwatar da makamancin ayyukan da ta yi a harabar filin wasan na Sani Abacha na samar da gine-gine a kewayan harabar Masallacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *