Mazabar Bichi ta yi dacen wakili

Mazabar Bichi ta yi dacen wakili

Mazabar Bichi ta yi dacen wakili

Tura wannan Sakon

Daga Usman Dangwari

Babu shakka, al’ummar mazabar tarayya ta Bichi sun kasance cikin rabauta daga ribar dimokuradiyya ta kowane fanni na kyautatuwar zamantakewar dan’adam, saboda kokarin da wakilin karamar hukumar watau Injiniya Kabir Abubakar Kabir wanda aka sani da (Abban Matasa).

A matsayi na na dan asalin karamar hukumar Bichi, zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana wani abu da ya dauki hankali na dangane da wakilcin Abban Matasa, tare da yin tsokaci kan irin alherai da wakilcin nasa yake haifar wa karamar hukumar Bichi.

Da farko dai na aminta cewa “Matasa” za su iya yin shugabanci mai kyau idan har suna samun dama a gwamnati duba da yadda  Kabir Abubakar Kabir yake ta kokarin ganin cewa, karamar hukumar Bichi ta zamo a sahun gaba wajen ci gaba ta fuskar ribar dimokuradiyya.

Sannan na hakikance cewa, wakilci abu ne mai amfani muddin dai ana kokarin samo wa al’umma ayyukan raya kasa ta yadda kowane mutum da ya yi zabe zai fahimci cewa, ya tura wakili jajirtacce wanda zai kare masa mutuncinsa da martabarsa a kowane lokaci.

Bisa haka ne nake amfani da wannan dama domin yin godiya ta musamman ga al’umar karamar hukumar Bichi da suka bai wa Abban Matasa damar yi masu wakilci ta yadda za’a gano irin kamun ludayin sa da manufofinsa wadanda ina ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu.

A gaskiya babu cikakken lokaci da zan iya bayyana dukkanin ayyukan alherin da Injiniya Kabir Abubakar Kabir ya yi wa al’umar mazabar tarayya ta Bichi ba, amma zan iya cewa, ya taba kowane fanni na zamantakewar al’umma kamar aikin hanyoyi da harkar ruwan sha da aikin haskaka garuruwa da kuma tallafawa ilimi.

Bugu da kari, Abban Matasa ya yi kokarin sosai  fannin kula da lafiya, sha’anin addini da kuma kyautata rayuwar matasa ta hanyar basu horo domin su kasance masu dogaro da kawunan su, wanda hakan zai ci gaba da amfanar al’umma lokaci mai tsawo.

Ni Alhaji Usman Dangwari, ina mai jaddada cewa, wakilin karamar hukumar Bichi a majalisar wakilai ta kasa ya ciri tuta bisa la’akari da yadda yake kai komo domin ganin al’ummar da yake wakilta sun kasance cikin yanayi mai kyau a tsari irin na dimokuradiyya wannan zamani.

Kafin in kammala sakon, zan yi godiya ga  zababben gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi na bunkasa jihar tare da kyautata yanayin siyasa wanda hakan ta sanya ake mutunta juna da ganin girman juna a tsarin siyasar jihar.

Daga karshe, Ina addu’a Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya a wannan kasa tamu, shugabannin mu kuma Ubangiji ya kara masu ikon ci gaba da yi mana jagoranci bisa adalci da sanin ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *