Mazauna Damboa dubu 30 sun amfana da tallafin Zulum –Rahoto

Gwamnan Borno, Babagana Zulum

Tura wannan Sakon

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar da kudi kimanin Naira miliyan 172 da kayan abinci, ga mazauna garin Damboa su fiye da mutane dubu 30.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar, Zulum da kansa ya shirya rabon kudaden da kayan abinci ga al’ummar garin, ciki har da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Gusau ya ce, an tantance mutane 436 wadanda suka rasa matsugunai da kayan abinci, sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a baya-bayan nan, da ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dama tare da raba wasu iyalai da muhallansu.

Bayan da shugaban karamar hukumar Dam­boa, Farfesa Adamu Aloma ya shaida masa barnar da ambaliyar ruwa ta yi, Zulum ya bayar da umarnin a bai wa kowane daga cikin mutane 436 tsabar kudi Naira dubu 50 da buhun masara hade da kayan sawa.

Gwamnan ya kuma jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya bukaci mazauna yankin da su daina gina gidaje a kan magudanar ruwa domin dakile abin da zai faru nan gaba.

Zulum ya kuma bayar da kyaututtukan da aka raba wa mutane 436 da ambaliyar ruwa ta shafa, ya kuma sa ido a raba Naira dubu biyar da yadudduka ga mazauna yankin fiye da dubu 30 wadanda yawa­ncinsu zawarawa ne, mata masu rauni da maza daga al’ummomi daban-daban.

Gwamnan a ziyarar da ya kai yankin, ya kuma zagaya unguwannin Hausari da tsohuwar kasuwar Damboa da Kachallaburari, tun da ya isa Damboa a ranar Lahadi.

A halin da ake ciki, gwamnan a lokacin da yake Damboa, ya bayar da umarnin rarraba taraktoci, ta hanyar tsarin rance, ga manoma.

Ya ce taraktocin za su kara habaka ayyukan no­man mazauna yankin, kasancewar su manoma.

A bangaren ilimi, Zulum ya duba hadaddiyar makarantar Islamiyya da ake ginawa domin hada ilimin addinin Islama da na zamani.

Ziyarar dai ita ce ta kara kaimi domin bai wa matasan da suka halarci makarantun Islamiyya sa­mun damar shiga manyan makarantu, domin samun kwatankwacin takardar shaidar difloma.

Tuni dai gwamnan ya amince da gina makarantu makamantan haka a garin Monguno bisa shirin sa­mar da makarantun a daukacin kananan hukumomi 27 na jihar Borno.

Idan aka yi la’akari da tarihin sama da shekaru dubu na karatun addinin Musulunci, Borno tana da dubban ’yan kasa da ke da ilimin addinin Musu­lunci.

Makarantun Islamiyya mafi girma suna bai wa irin wadannan ‘yan kasa, wadanda suka cika wasu sharudda, damar da za su iya samun shiga makaran­tun hadin gwiwa, inda suke samun kwatankwacin shaidar Difloma da za su iya neman karin ilimin za­mani domin zama masu Digiri domin samun ci gaba matuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *