Mbappe ya ragargaza ragar Barcelona a Nou Camp

Tura wannan Sakon

Paris St Germain ta casa Barcelona da ci 4-1 a gasar Champions League wasan farko karawar zagaye na biyu da suka fafata ranar Talata a Nou Camp.

Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a ragar PSG wadda ta buga wasan karshe a bara a gasar da Bayern Munich ta doke ta 1-0.

Bayan da Messi ya fara cin kwallo a minti na 27 da fara tamaula, PSG ta kara sa matsi, inda ta farke ta hannun Kylian Mbappe, san­nan ya kara na biyu.

Dan kwallon Eberton, Moise Kean da ke buga wasa aro ne ya kara ci wa PSG kwallo, kuma na uku a fafatawar da ya bai wa kungiyar da ke buga Ligue 1 kwarin gwiwa.

Barcelona ta yi ta kai kora don ta zare kwal­layen da aka zura mata, amma hakan bai yiwu­ba, sai PSG ta kai wata kora kuma Mbappe ya ci na hudu kuma na uku a wasan.

Barcelona za ta ziyarci Faransa ranar 20 ga watan Maris domin buga wasa na biyu da ake sa ran watakila Neymar ya warke ya kuma fus­kanci tsohuwar kungiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *