Messi Ya Ci Wa Kasarsa Kwallaye 100

Tura wannan Sakon

Daga Hassan Muhammad

Lionel Messi ya ci wa Argentina kwallo na 100, a wasan sada zumunta da tawagar ta doke ta Jamaica 3-0 a tsakar daren Talata.

 Wannan nasarar ta sa Argentina ta yi wasa 35 a jere ba tare da an doke ta ba, saura biyu ta yi kan-kan-kan da Italiya, mai tarihin wasa da yawa a jere ba tare da rashin nasara ba a duniya.

Dan wasan Manchester City, Julian Albarez ne ya fara ci wa tawagar da Lionel Scaloni ke jan ragama kwallo, bayan da ya samu tamaula ta hannun Lautaro Martinez.

Messi mai shekara 35, wanda ya shiga fafatawar daga baya ya ci kwallo biyu daya a bugun tazara. Dan wasan Paris St Germain ya ci wa Argentina kwallo na 100 a wasa 164, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Kudancin Amurka, shi ne na uku a duniya.

Wasan sada zumunta da Argentina ta yi a New Jersey daga nan sai shirin zuwa Katar, domin buga gasar Kofin duniya da za a fara ranar 21 ga watan Nuwamba. Wadda take da kofin duniya biyu da ake sa ran za ta iya daukar a shekarar nan, za ta fara karawa da Saudi Arabia ranar 22 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *