Mika ragamar mulki: Tambuwal ya yi layar zana

Musa Lemu Daga Sakkwato
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Barista Aminu Waziri Tambuwal ya sa kafarsa ya fice ya bar jihar a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu 2023 ba tare daya mika kundin mulki ga zababben gwamnan jihar Ahmad Aliyu Sakkwato ba.
Gwamna Tambuwal ya gudu ya bar Sakkwato ba tare da tura wakili ko kuma wani babban jami’ in gwamnati da zai wakilce shi a ranar 29 ga watan Mayu 2023 ba domin ya mika mulkin ga zabab-ben gwamna ba.
A yayin da yake jawabi jim kadan bayan karbar rantsuwar kama aiki daga babban mai shari’a na jihar, Muhmmad Sa’id Sifawa gwamna Ahmad Aliyu ya ce, gwamnatinsa za ta yi kokari wajen tabbatar da cika alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.
Sabon gwamnan, dan shekaru 53 ya ce, gwamnatinsa za ta bayar da fifiko ta fannin tsaro da inganta rayuwar al’ummar jihar sannan samar da ayyukan yi ga matasa kazalika da ruwan sha tare da inganta harkokin ilimi da noma.
Ya ce, gwamnatinsa za ta hada hannu da gwamnati tarayya domin ciyar da jihar gaba ta fuskar bunkasa tattalin arziki da raya karkara.
Ya ce, ma’aikata za su dara kazalika da wadanda suka yi ritaya ganin yadda gwamnatin Aminu Tambuwal ta yi watsi da su ba tare da ba su hakkokinsu ba.
Hakika tarihi ya nuna cewa, a shekarar 2007 mulkin gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa mataimakinsa Abdullahi Ciso Dattijo shi ne wanda Bafarawa ya umurce shi da ya mika mulki ga zababben gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko a inda shi ma Wamakko ya mika mulkin ga Aminu Waziri Tambuwal a shekarar 2015.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ce, mazauna karkara ba za a bar su baya ba wajen tabbatar da an samar da takin zamani a kan lokaci domin samar da wadataccen abinci a jihar da kasa gaba daya.