Ministoci masu son yin takara, a ajiye aiki –APC

Ministoci masu son yin takara, a ajiye aiki –APC

Shugaban APC Abdullahi Adamu

Tura wannan Sakon

Domin kauce wa taka dokar zabe ta Nijeriya, jam’iyyar APC ta bayyana ranar karshe da ministoci da masu rike da mukaman gwamnati ya kamata su ajiye ayyukansu a matakan tarayya da na jihohi idan suna son tsayawa takara a zabbukan da ke tafe. Jami’an gwamnatin na da zuwa ranar Asabar 30 ga watan Afrilu su ajiye mukaman nasu.

Matakin ya shafi wadansu ministocin gwanatin Buhari kamar ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da kwadago Chris Nigige, suna ciki jami’an da suka bayana aniyarsu ta tsayawa takara.

Sashe na 3(i) na dokar jam’iyyar APC kan tsayar da ‘yan takara a zaben 2023 na cewa: “Ba a yarda wani jami’in da ke rke da mukami a kowane matakin gwamnati ya zama deleget ko a zabe shi domin fitar da ‘yan takara.”

Jadawalin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar ya tsara cewa, jam’iyyun siyasa na da zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin su mika ma hukumar mutanen da suka tsayar a zabbukan da ke tafe.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *