Misau ta karbi bakuncin USAID kan tattalin arziki

Misau ta karbi bakuncin usaid kan tattalin arziki

USAID

Tura wannan Sakon

Shugaban karamar hukumar misau, Alhaji Abubakar Ahmad (Garkuwan Misau) ya karbi bakuncin wata tawaga daga ma’aikatar kungiyar USAID domin bai wa karamar hukumar Misau gudumawarsu.

A nasu bangaren gurin habaka tattalin arzikin yankin da kuma bai wa ma’aikata bita ta musamman domin inganta aikin gwamnati a karamar hukumar Misau.

Shugaban karamar ya bayyana farin cikinsa da ziyarar tare da nuna godiyarsa ga ma’aikatar USAID domin irin gudumarwar da take bayar wa a dukkan fadin kasar nan tare da yaba wa ma’aikatan karamar hukumar yadda suke ba shi hadin kai domin ciyar da karamar hukumar gaba.

Shi ma shugaban sashen kasafin kudi da tsare tsarensu, Alahaji Musa Idris (Dan Malikin Dambam) ya nuna farin cikinsa da bakin na alheri tare da jan hankalin ma’aikatan karamar hukumar Misau gurin ba su hadin kai, domin morar aikin kamar yadda suka bayyana cewa, a jihar Bauchi da kananan hukumomi 7 ne suka samu wannan dama karamar hukumar Misau tana daga cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *