Mu’assatul Abdulwahab, Tudun-Jukun ta tallafa wa marayu 115

Mu’assatul Abdulwahab, Tudun-Jukun ta tallafa wa marayu 115

Mu’assatul Abdulwahab, Tudun-Jukun ta tallafa wa marayu 115

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

A farkon wan­nan makon ne gidauniyar tal­lafa wa al’umma marasa karfi da kuma marayu, wadda ake kira da sunan MU’ASSATUL ABDUL­WAHAB ISLAMIC CEN­TRE wadda ke Unguwar Tudun Jukun a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, ta tallafa wa ma­rayu maza da mata har su 155 da kayayyan abinci da kuma marayu maza da mata, taron rabon rarraba kayayyakin da kuma tu­fafin ya gudana ne a bisa shugabancin babban da­raktan gidauniyar Alhaji Bala Alba – Bello a bab­ban masallacin day a gina.

A jawabinsa wajen ra­bon kayayyakin da aka aambata, Alhaji Bala Alba – Bello, ya farad a cewar, wannan taron bas hi ne na farko ba, domin ka­mar yadda y ace an shafe shekaru da dama wajen ai­watar da wannan tallafi ga marayu da kuma al’umma maza da mata, wanda a wannan shekara an tallafa wa al’ummomin da aka ambata inda maza marayu 55 da kuma mata 60 suka sami tallafin da aka bayy­ana.Alhaji Alba- Bello ya yi kira ga al’umma da su rika tallafa wa marayu da kayayyakin abinci da tu­fafi domin su sami damar das u ma za su gudanar da rayuwarsu, kamar yadda sauran al’umma ke yi, ba lallai sai lokacin azumi ko kuma lokutan sallah ba, a cewarsa, tallafa wa mara­ya, a kwai ;ada mai yawan gaske daga mai kowa mai komi, wanda mutum zai fara ganin sakamako tun a nan duniya kafin gobe.

Da kuma ya juya ga mawadata, sai ya sake kira garesu na su rika wani bangare na dukiyansu, do­min tallafa wa marayu da sauran al’umma da suke bukatar tallafin abin da za su ci tare da iyalansu, duk mai yin wannan, kamar yadda Alhaji Alba – Bello ya nanata, zai ci gaba da ganin haske a rayuwarsa, baya ga fadadan dukiyar­sa da zai gani a dan kan­kanin lokaci.

Sauran wadanda suka yi jawabin a wajen rabon kayayyakin sun hada da Dokta Shehu Umar daya daga cikin ma su wukar yankar magana a gidauni­yar da kuma babban li­mamin masallacin Juma’a na Alba – Bello, Dokta Hamza Al- Sudani da sau­ran malamai ma su yawan gaske.

A dai lokcin wannan taro, an rarraba tufafi da suka hada da Atamfa da takalma da sada kayayya­kin binci da suka hada da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *