Mukabala: Kungiyar NACOMYO ta jinjina wa gwamnati

Mukabala
Daga Salisu Baso
An jinjina wa matakin gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam) saboda bayar da damar tattaunawar ilmi tsakanin gamayyar Malamai da kuma Malam Abduljabbar Nasiru Kabara domin ba shi damar kare kansa kan kalaman da ya furta da suka danganaci martabar Manzon Allah SAW da sahabbansa masu daraja.
Shugaban majalisar kungiyoyin matasan Musulmi ta kasa (NACOMYO) reshen jihar Kano, Malam Ahmad Abubakar Mai zube ya bayyana jin dadinsa a ganawarsa da manema labarai a karshen taron kungiyar na yankin Arewa a jihar Kano, a makon da ya gabata.
Ya kuma gode wa kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin Addinai, Dokta Muhammad TahirAdam Baba Impossible da shugabanni da ma’aikatan hukumar Shari’a ta jihar da kuma hukumomin tsaro saboda jajircewarsu wajen ganin an yi mukabalar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Majalisar ta yi jan hankali ga dukkanin matasa masu kokarin neman ilmi addini da su kasance masu kula da malaman da suke neman ilmi a gabansa domin gudun fadawa cikin munana akidu masu rikitarwa.
A karshe, majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta hanzarta daukar matakin da ya da ce a kan wanda ya furta munanan kalamai ga Manzon Allah (SAW) da sahabbansa domin zama darasi ga na