Mukhtar Ishak ya sha yabo -Saboda tallafa wa ilimi

Tura wannan Sakon


Daga Hassan Falaki Kulkul

A karshen makon jiya, ranar Asabar, aka yi bikin yaye dalibai na makarantar BIT ta koyon sarrafa na’ura mai kwakwalwa da ke jihar Kano, a karkashin jagorancin gidauniyar Mukhtariyya.

Taron wanda aka gabatar a makarantar Maryam Aloma Mukhtar da ke Kofar Nassarawa.

An yaye dalibai sama da 6300, wadanda suka sami ilimin Difloma da babbar Difloma, hadi da mata wadanda suka koyi sana’ar daukar hoto su 500, sai kuma aka tallafa wa masu sana’ar sayar da awara da masu sana’ar yin shayi da masu lalura ta musamman, wadanda suka rabauta da jari domin bunkasa sana’o’insu.

Tun da farko, da yake nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Alhaji Fa’izu Kamaluddeen Adamu Namaji, ya yaba wa Alhaji Mukhtar Ishak Yakasai, shugaban gidauniyyar Mukhtariyya, bisa irin ayyukan alheri da yake gudanarwa, da kuma goyon bayan da yake bai wa mai dakin gwamnan Kano, Farfesa Hafsa Ganduje.

Daga nan ya mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka halarci taron.

Da yake nasa jawabin, shugaban makarantar, Malam Muntaka Mukhtar Ibrahim ya mika godiyarsa da yabawa da kuma nuna jin dadinsa ga shugaban gidauniyar Mukhtariyya bisa daukar nauyin wadannan matasa domin su samar wa kansu abin dogaro da kai da kuma bunkasa sana’o’i na kaka da kakanni.

Ya kuma bayyana cewa, wannan gagarumin aiki da ya shafe shakara biyar yana yi, inda ya bayyana cewa, wannan wani jan aiki ne da sai manyan bayin Allah ne suke yin sa.

Daga nan sai ya gode wa mai dakin gwamnan Kano, bisa irin goyon bayan da take bayarwa na halartar irin wadannan tarurruka na makarantu, inda ya kwatanta Farfesar da cewa, ta zama agogo sarkin aiki, ba dare ba rana, aiki kullum ta na tafe wajen tallafa wa al’ummar jihar Kano.

Daga nan ya hori daliban da aka yaye, da su kasance masu sadaukar da kansu wajen ci gaba da zama jakadu nagari da kuma aiki da abin da suka koya.

Shi kuma a nasa jawabin, shugaban gidauniyar, Alhaji Mukhtari Ishak Yakasai, ya kara gode wa mai dakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsa Umar Ganduje, bisa irin gudummawar da take bai wa kungiyoyin taimakon al’umma, sannan ya kara da cewa, ya yi koyi ne da gidauniyar Ganduje, wadda take taimakon al’umma.

Yakasai ya ce, gidauniyar, harsashinta shi ne gyaran makarantu da gina makarantu da gyaran rijiyoyi da gyaran masallatai da gyaran makarantun allo da samar wa masu bukata ta musamman aikin yi da tallafa wa marayu da sauran abubuwan ci gaban al’umma, Da take nata jawabin, mai dakin gwamnan Kano, Farfesa Hafsa Umar Ganduje, ta yaba da irin aikin da gidauniyar ta Mukhtariyya take yi tsawan shekaru biyar na bai wa dalibai 6303 da kuma bayar da jari ga masu sana’ar hannu.

Ta kara da cewa, irin wannan aiki na al’umma yana rage wa iyaye da gwamnati nauyi, daga nan ta bayyyana Mukhtari Ishak Yakasai da cewa, “Mukhtari danmu ne, yaronmu ne, mai aikin da yake yi ta karkashin gidauniyarsa, wannan shi ne aikin gidauniyar Ganduje” A karshe, an rarraba wa masu shayi da masu awara da masu bukata ta musamman tallafin jari.

Ita kuma makarantar ta BIT an ba ta kyamarori guda ashirin domin ci gaba da koyar da dalibai karatun daukar hoto. Taron ya sami sanya albarka daga manyan baki irin su, kwamishiniyar ilimi mai zurfi da kwamishinan shari’a da shugaban APC na jihar Kano da shugabannin kananan hukumomin Kumbotso da Ungoggo da Alkali Alhaji Hamza Darma.

kaunarmu ne kuma da ne mai biyayya a gare mu, saboda haka, muna godiya a gare shi, bisa irin aikin da yake yi ta karkashin gidauniyarsa, wannan shi ne aikin gidauniyar Ganduje”

A karshe, an rarraba wa masu shayi da masu awara da masu bukata ta musamman tallafin jari.

Ita kuma makarantar ta BIT an ba ta kyamarori guda ashirin domin ci gaba da koyar da dalibai karatun daukar hoto.

Taron ya sami sanya albarka daga manyan baki irin su, kwamishiniyar ilimi mai zurfi da kwamishinan shari’a da shugaban APC na jihar Kano da shugabannin kananan hukumomin Kumbotso da Ungoggo da Alkali Alhaji Hamza Darma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *