Mulki ba ya dorewa da zalunci – In ji Dan Pass

Alhaji Gambo Dan-pass

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Wani hamshakin dan kasuwa kuma jagora a siyasar Nijeriya, basarake, Alhaji Muhammadu Gambo Dan Pass (Dan Saran Kano) ya ce, ya kamata shugabanin kasa su ji tsoron Allah, kuma su tuna cewa, Allah zai tambaye su a kan yadda suka gudanar da shugabancinsu ga al’umma.

 Ya bayyana cewa, tabbas mulki ba ya dorewa da zalunci. Yanayin da ake ciki yanzu abin tsoro ne, kuma abin takaici ne.

 Dan Pass ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke kasuwar Kantin Kwari, a birnin Kano, a makon da ya gabata.

Ya ce, ganin yadda yanayin harkokin kasuwanci ya yi koma baya, talauci ya yi katutu a tsakanin al’umma, rashin tsaro ya zama ruwan-dare, rashin aikin-yi ga matasa kullum karuwa yake yi, don haka mafita a nan ita ce, dole a koma ga Allah, kuma a rungumi Istigfari da Salatin Annabi.

Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar APC da ke mulki, ta rugurguza tattalin arzikin kasar nan rugu-rugu, idan har ba a dauki mataki ba, ba shakka za a ci gaba da fuskantar koma baya, musamman wajen harkar kasuwanci da harkar ilimi da kuma tsaro.

 Ya ce, jam’iyyar APC ta gaza cika dukkanin alkawarirrikan da ta yi wa al’umma, saboda haka ne mutane suke tururuwa zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, domin ita ce mafita a Nijeriya.

 Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya cewa, yanzu dama ta samu, kuma dabara ta rage ga mai shiga rijiya, jama’a su fito kwansu da kwarkwatarsu domin neman yancinsu wajen zaben jam’iyyar NNPP, domin ita ce kadai jam’iyya a kasar nan wadda za ta kai al’umma tudun-mun-tsira.

Daga karshe ya bai wa shugaba kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso wajen jajircewarsa da ganin talakawa sun sami ‘yanci a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *