Mun dauki nauyin karatun yara fiye da 50 -Sanusi Hashim

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sunusi Kano

Fiye da yara dubu 3 ne suke samun tallafin karatu daga gidauniyar taimaka wa yara da marayu domin sama masu gata kamar sauran yara a jihar Kano.

Wannan na zuwa ne daga bakin babban daraktan gidaunyar taimaka wa yaran ta bangaren ilimi da marayu, Kwamred Sanusi Hashim a wata zantawa da wakilin Albishir ranar Litinin.

Daraktan ya bayyana cewa, suna da bangarori daban-daban a tafiyar ta su kama daga sashen ilimi da sashen da ke kula da matsalolin mata da sauransu. Kazalika ya tabbatar da cewa, kasancewar halin da unguwannin mu suke ciki a yanzu na daya daga cikin abin da ya sa suka samar da gidauniya.

Shugaban ya kuma cewa, suna fatan nan ba da dadewa ba za su karade sauran jihohin Arewa kasancewa yanzu sun fara tsallaka wa karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa, inda suka fara da bayar da kayan makaranta da littattafai da sauransu.

Haka kuma ya bukaci gwamnati da ta mayar da hankali kan kungiyoyi sahihai wadanda suka cancanta domin gudanar da aiki tare, kazalika ya kuma kara mika bukatarsu ga gwamnati wajen ganin ta kara kaimi duk da kasancewar tana bakin kokarinta. Shi ma daraktan ayyuka na gidauniyar, Malam Turadu Surajo ya ce, akwai ayyuka da dama da suke kai yanzu haka bayan wanda suka gabatar a baya.

Turadu ya ce, ayyukan sun hada da kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki, sai taimaka wa masu tarin tb, sai masu cutar zazzabin cizon sauro, sai kuma akwai yara masu zaman kansu da sukan fuskanci matsala wanda sukansa ido domin ganin wani abu bai same su ba.

Sai batun koya wa yara karatu bayan dawowa makaranta, sai sa’ido ga matasan da suka tsinci kansu ga harkar shaye-shaye sukan duba yadMun dauki nauyin karatun yara fiye da 50 -Sanusi Hashim da za su taimaka masu.

Ya kuma ja hankalin iyaye wajen rashin tura yaransu koyan sana’ar hannu, inda ya ce, ba wai sai an ci abinci da karatun boko ba akwai hanyoyin cin abin da yawa a yanzu.

Ita ma Rahila Ibrahim da ke kula da sashen matsalolin mata kama daga ciwo har ba su tallafi ta bayyana cewa, akwai matan da suka yi karatu amma babu aiki domin haka suna bin hanyoyin da ya dace, domin sama masu ga ta da tamaiko Sai kuma daukar matakin wadanda suka gabatar da fade ga yarinya, kuma sukan taimaka wa yaran da abin ya faru da su tare da taimako na musamman.

Rahila ta bukaci mata su yi hankali wajen neman ilimi na addini da zamani, ta kuma bukaci gwamnati da masu hannu da shuni kan shigowa domin su saka jarinsu. Kazalika gidauniya ta yi kokarin talllafa wa matan da ke gidajensu da dabbobi domin kiwata wa tare da magance matsalolin zaman banza tare da kaucewa wulakancin wadansu mazajen a gidajensu.

Daga karshe, sun bayyana cewa, suna bakin kokarin koyawa mata yadda za su zama masu tattali na yau da gobe ba tare da tsangwama ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *