Mun gamsu da zaben kananan Hukumomi a Kano -Sa’adu Hayin Hago

zaben kananan Hukumomi a Kano
Tura wannan Sakon

Jabiru A Hassan, Daga Kano

Wani jigo a jam’iyyar APC Alhaji Sa’adu Mukhtar Hayin Hago ya nuna gamsuwar sa bisa yadda zaben kananan hukumomi ya gudana a jihar Kano a ranar Asabar 16 ga Janairun wannan shekara inda ya jaddada cewa, nasarar da jam’iyyar ta samu ya yi nuni da cewa, al’umma sun aminta da yadda take tafiyar da mulki a matakai daban-daban.

Ya yi tsokacin a hirar su da wakilin mu a mazabar a Marke lokacin da ya duba yadda zabe ke tafiya a mazabar, tare da bayyana cewa, ko shakka babu, jam’iyyar APC ita ce kadai take da kyawawan tanade-tanade na alheri ga al’ummar wannan kasa musamman ganin irin nasarorin da ta samu cikin shekarun da ta yi tana mulki a kasar nan.

Alhaji Sa’adu Hayin Hago ya sanar da cewa, shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje shugabanni ne wadanda suke kokari dare da rana domin ganin kasarnan tana samun ci gaba mai albarka ta kowane fanni, sannan ya yi tsokaci kan yadda al’ummar Nijeriya suka fahimci cewa, mulkin APC ya kawo sauyi a kasarnan duk da irin kalubalen da duniya ke ciki.

Ya ce yana da kyakkyawan za to cewa, zababben shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa watau Alhaji Ado Tambai Kwa da Kansilolinsa 11 za su ci gaba da aiwatar da managartan ayyukan alheri a fadin karamar hukumar musamman ganin yadda suka yi a zango na farko, tare da mika sakon fatan alheri ga dukkanin zababbun da Allah ya bai wa nasara, inda ya bayyana cewa, zai ci gaba da bayar da tasa gudunmawar ta yadda al’amura za su kara yin kyau.

A karshe Hayin Hago ya jinjina wa gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen bunkasa jihar Kano tare da kyautata yanayin siyasar jihar kamar yadda tsarin dimukradiyya ya tana da, inda ya bukaci matasa da su ci gaba da kasance wa masu bin dokokin kasa da dogaro da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *