Mun karbi faduwar Pdp da dattako – In ji Gwamnan Bauchi

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau Daga Bauchi

Gwamna Bala Muhammad Abdulqadir na jihar Bauchi ya bayyana jin dadinsa da godiyarsa ga daukacin mambobin PDP da goyon baya da yarda da rashin nasara da aka yi a jam’iyyar PDP na zaben da ya gudana na cike gurbi na Majalisar jiha a Dass mun karbi faduwa da mutunci da dattako.

Gwamnan ya bayyana rashin samun nasarar jam’iyyar PDP a matsayin  haka Allah yaso, ya kuma qara qarfafa gwiwa ga membobin jam’iyyar kar wannan yasa a samu rarrabuwar kai da koma baya.

Gwamna Bala Muhammad Abdulqadir ya bayyana rashin samun nasarar a matsayin darasi ne ga mu duka da gwamnati da jam’iyyar PDP muna da buqatar yin tsare-tsare domin riqe martabar jam’iyyar da hikimomi da dabaru da kuma aiki a tare.

“ Dukkan godiya ya tabbata ga Allah, rashin nasarar jam’iyyar mu tabbas darasi ne a garemu duka, babu wanda za mu yi zargi a kan haka.

“Idan za ku iya tunawa mun rasa kujeru 21 na Majalisar dokoki da Sanatoti guda Uku a 2019 amma Allah ya ba mu sa a muka ci zaben gwamna, kar mu zargi kowa a cikin wannan al’amari, mu barshi a cikin gida, banda cece-kuce, da rashin yarda da juna”

Gwamna Bala Muhammad Abdulqadir ya bayanna farin cikinsa ga duka mambobin jam’iyyar PDP na bayar da goyon bayansu da gudunmawa na ganin an samu nasarar gwamnatinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *