Mun yi kokarin kashe gobara a kasuwar Lahadin-makole -PFO Sa’eed Muhammad

PFO Sa, eed Muhammad Ibrahim

PFO Sa, eed Muhammad Ibrahim

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi

J ami, in hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar jihar Kano PFO Sa’eed Muhammad Ibrahim ya ce Jami, ansu sunyi kokari sosai wajen kashe gobara a kasuwar lahadin Makole a ranar talata da ta gabata misalin karfe biyu na Rana Sa, eed Muhammad ya ce sun sa mi labarin tashin wutar ne ta bakin wani bawon Allah mai suna Malan Nura Isyaku, wanda cikin kankanin lokaci muka tura Jami, anmu da ke karamar tashar mu ta Danladi Nasidi wanda suka isa wannan kasuwa da lamarin ya ke aukuwa tana cin wuta a lokacin, amma cikin ikon Allah sun samu damar shawo kan wutar tare da kasheta.

Sa, eed Muhammad Ibrahim ya ce alhamdulillah a wannan gobara babu asarar rai ko wani yaji rauni da ya samu wani, sai dai hukumar kashe gobara ta jihar Kano na amfani da wannan da ma wajen kira ga Al, umma da su rinka kiyaye wa wajen yadda suke amfani da wuta domin kare kai daga gobara.

A wani labarin kuma humukar kashe gobara ta jihar Kano karkashin jagoarancin Alhaji Hassan Ahmad Muhammad ta karbi kiraye-kiraye da ya shafi hatsarin gobara da na neman agaji na ceto daga tashoshinta daban-daban da ke birnin da kauyukan jihar cikin wannan wata na junairu da ya kare.

PFO Sa, eed Muhammad Ibrahim Jami, in hulda da jama, a na hukumar ya ce cikin wannan wata daya gabata hukumar ta sa mu kiraye-kiraye na ceton rayuka da dukiyoyin Al, umma daga hatsarin gobara akalla guda 98, sai kira 72 da ya shafi neman agaji, sai kira wanda ba na gaskiya ba guda 16.

Sa, eed Muhammad Ibrahim ya kara da cewa akalla an rasa dukiya a wannan wata na junairu sakamakon hadarin gobara da sauran hadarurruka, wanda ya kai kimanin naira miliyan ashirin da bakwai da dubu dari uku da hamsin, sai kuma dukiyar da aka ceta wadda ta kai kimanin naira miliyan arba, in da tara da dubu dari shida, sannan an sa mu asarar ruyuka na mutane sakamakon hadarurruka da suka auku a wannan wata na junairu guda 7,sai rayukan mutanen da aka ceta har mutum 99 a hadarurruka da daban-daban.

Wanda a karshe a madadin mai girma darakta Hassan Ahmad Muhammad mu na amfani da wannan da ma wajen kara kira ga Al, umma da su rinka kiyaye yadda suke amfani da wuta domin kare aukuwar hadarin gobara, sannan a rinka bin doka da ka, idojin hanya yayin da ake tuki a kan tituna domin kare kai daga hadarin mota akan hanyoyi, sannan ya na da kyau iyaye su tabbatar sun hana ‘yayansu zuwa wasanni ko wanka a bakin rafuka da kududdufai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *