Mun yi rashin mai Kashiful Gummati

Mun yi rashin mai Kashiful Gummati

Mai Kashiful Gummati

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad S.Ahmad

Shahararren mutumin nan a birnin Kano, Malam Kabiru Usman wanda ake yi wa lakani da mai Kashiful Gummati da ake yawan jin sa a kafafen yada labarai a duk lokacin da Marigayi Sheikh Isa Waziri ke gudanar da Tafsirin Alkur’ani ya kwanta dama.

Malam Kabiru ya rasu yana da Shekaru 74 kuma bar matarsa da ‘ya’ya 8 sai jikoki 40.

Marigayin ya rasu ne a ranar Talata 30 11 2021 har yanzu kuma mutane na ta tururwa zuwa gidansa da ke unguwar Sanka cikin birnin Kano domin yi wa iyalansa ta’aziyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *