Mustapha Usman ya zama sarkin Bargu Ka’oje (I)

sarkin Bargu Ka’oje (I)

Tura wannan Sakon

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Dubun dubatar mutane ne suka halarci nadin sarkin Bargu Ka’oje Alhaji Mustapha Usman Adamu, sarki na 13 a tarhin masarautar.

Tarihi ya nuna cewa an kirkiro garin Ka’oje ne a shekara ta 1823, (watau kimanin shekarru 200 da suka wuce) lokacin da Mallam Abdullahi Fodiyo, Sarkin Gwandu na farko (1) a karkashin Daular Usmaniyyah, ya umurchi wani Bahillace, Jarumin Mayaki, mai suna Yakuba Ibn Sakita, da ya assasa gari a yankin karshe na yammanchin Daular Usmaniyyah. Bisa ga wannan umurni ne aka assasa garin KA’OJE a shekara ta 1823,

kuma Yakuba Ibn Sakita shine sarki na farko, da aka kira da lakabin SARKIN BARGU KA’OJE. Dashi da kanenai, mai suna Zangi Ibn Sakita, suka yi mubayi’a ga Masarautar Gwandu. Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ‘ya ‘yan Yakuba Ibn Sakita ne ke rike da wannan sarauta ta SARKIN BARGU KA’OJE.

Wannan nadin sarauta na Alhaji Mustapha Usman Adamu a matsayin Sarkin Bargu Ka’oje na goma sha ukku (13) nuni ne ga irin mubayi’a da kauna wadda Masauratar Bargu take wa Masauratar Gwandu mai darajja. Garin Ka’oje yana da tarihi mai dinbin yawa.

A can da, yankin kasar da aka cema Ka’oje yanzu, yanki ne mai girma da ba ya da mutane da yawa. ‘Yan kalilan mutane da ke zaune a wurin, kabilolin Kengawa ne da Gungawa.

Wadannan kabilolin sun kasanche kanana ne, kuma suna rarrabe dabam dabam a mashayar Tekun Kwara, wadda aka fi sani da Riber Niger.

A farkon karni na goma sha tara (19th century), Jarumman Fulani da suka yo hijira domin mubayi’a ga Mallam Shehu Usman Danfodiyo da kane nai, Mallam Abdullahi, da kuma bada gudummuwar su ga yakin jihadin Daular Usmaniyyah, sun fara zama ne a wani gari mai suna Gulumbe.

Amma saboda hare-haren yaki na Malukiyar Borgu, wadda ta kunshi Bussa, Illo da Nikki, Mallam Abdullahi ya umurchi Jarumman Fulani su ketari Tekun Kwara domin su kafa gundumar da zata kare Daular Usmaniyyah daga hare-haren yaki da Shugabannin Mulkin Borgu su keyi.

Aikin farko da suka gabatar bayan sun sauka a yankin Ka’oje, Jarumman Fulani sunyi gyare-gyare akan tafiyar da al’amurra na mulki da na rayuwa a dukkan kauyukkan wannan yanki, da suka hada da Kengawa da Gungawa, domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sun fadada yankin Ka’oje har cikin kasashen Mulkin Borgu. Kuma bisa ga burin Mallam Abdullahi Fodiyo, sun tabattadda cewa yankin Ka’oje ya zama ginshiki ga duk wani azzalumi mai son ya kaima Daular Usmaniyya yaki. Saboda la’akari da namijin kokarin Jarumman, jama’ar yankin suka yarda bakin Fulani su kasance shugabanni a wadannan kasashen.

An samu nasarar wadannan gyare-gyaren mulki matuka har ya kasance Mallam Abdullahi Fodiyo, domin ya karfafa mulkinai a Masarautar Gwandu ta Daular Usmaniyyah, ya tabatadda mulkin Jarumman Fulani a wannan yanki.

Yana da kyau a fahimci cewa Jarumman Fulani sun bari wadannan kauyukka dake rarrabe a mashayar Tekun Kwara su zauna da shugabanninsu ba tare da an tsangwame su ba, kuma suyi mubayi’a kai tsaye ga Masarautar Gwandu. Don haka, wannan gunduma wadda ta kunshi kauyukka da dama, hadda kasar Jarumman Fulani, ta zama yanki mai darajja wadda aka sama suna Gundumar Bargu.

Bisa ga haka ne aka kirkiri sarautar SARKIN BARGUN KA’OJE bayan Mohamman, wanda daga baya yazzama Sarkin Gwandu na biyu, ya ko karta wajen sasanta shugabanin Fulani na Bargu da Sarkin Kengewa, Sarki KI-TAKU, domin su zama gunduma guda a karkashin Masarautar Gwandu. Ka’oje, gari ne wanda yayyi suna a wajen zaman lahiya tun lokacin da anka kirkiro shi. Akasarin gefen garin Ka’oje daga Kudu har zuwa Yamma, gonakki ne.

Amma a Arewacin Ka’oje, akwai kananan kauyukka wadanda aka yi musu katanginne domin kare su daga hare-haren da Shugabannin Mulkin Borgu ke kaiwa akai-akai.

Tarihi ya nuna cewa hari na karshe da Shugabannin Mulkin Borgu suka kaima Ka’oje ya faru ne a shekarar 1861, lokacin da sojojin Sarkin Bussa suka kama garin Gendane, kuma suka zauna a wurin, wata da watanni, domin shirin kaima Ka’oje hari. Amma sojojin Sarkin Bargu Mallam Buhari, suna rike da Kwari da Baka, a karkashin Sarkin Yaki Amah da Daudu Musayi sun fatattaki sojojin Sarkin Bussa.

Ya kamata a san cewa, soyayya da girmamawa dake tsakanin Masarautar Gwandu da Ka’oje tassa Sarkin Gwandu yabbada jarummai mahayan dawakai 70 domin su taimaka ma Jarumman Sarkin Bargu Buhari a wannan yaki. Jarumman Sarkin Bargu Buhari sun samu nasara sosai har yassa Sarkin Bussa ya gudu daga Gendene babu ko shiri.

Lokacin da sojojin Ka’oje suka dawo gida, gari ya dauki ciri, ana murna, ana kirari cewa, “Ka’oje Garin Baka ta Buhari; Namiji Baka; Macce Baka; Kai ko kadangare da Baka tai!” Tun lokacin da sojojin Sarkin Bussa sunka tsere ba shiri a shekarar 1863 har zuwa lokacin mulkin mallaka da iya zuwa yau, gundumar Ka’oje ta kasance mai zaman lafiya, kuma jama’ar ta suna sana’o’insu cikin kwanciyar hankali da wadata.

Sana’o’in da sukayi fice cikin gundumar Ka’oje, a lokacin da, sune kiwon dawakai, kimar dabbobi da kuma noma. Jama’a sun sami nasarori kwarai da gaske a wadannan sana’o’i saboda Tekun Kwara mai ruwan albarka. Kuma ga babbar kasuwar Bidda inda jama’a ke safarar dawakai da dabbobi da kayan abinci.

Ka’oje kam tun lokacin har bisa yanzu, ba za’a ce komi ba sai Alhamdulillahi! Wannan zaman lafiya da wadata a kasar Ka’oje shine dalilin da yassa tassami Sarakuna guda goma sha ukku (13) cikin ruwan sanyi in an hada da Sarkin Bargu Ka’oje na 13, Alhaji Mustapha Usman Adamu.

Sarkin Bargu Ka’oje na farko shine Yakuba Ibn Sakita, wanda yayyi mulki tsakanin shekara 1823 da 1848; Sarkin Bargu na biyu shine Sarkin Bargu Muhammadu Zangi, wanda zamani nai yaffara a shekarar 1848 da 1851; Sarkin Bargu na ukku wanda yayyi zamani har zuwa shekarar 1851 da 1865 shine Sarkin Bargu Ibrahim Zangi.

Sarkin Bargu na hudu (4), Mallam Buhari (1865 – 1905) shine yayyi tsawon mulki, kuma tun bayan rasuwa tai, ‘ya‘ya nai da jikoki nai suke sarautar Sarkin Bargu Kaoje.

Ga jerin sarakunan da Bargu tayi Nan kar yadda Alhaji Nuhu Sani ya sanarwa wakilin mu Kamar haka Sarkin Bargu na farko cikin ‘ya‘ya da jikokin Mallam Buhari shine Sarkin Bargu na biyar (5), Muhammadu Buhari (1905 – 1914), kuma shine Kakan wannan Sarkin Bargu Ka’oje na 13, Alhaji Mustapha Usman Adamu.

Sauran Sarakunan Bargu Ka’oje da akayi sune Sarkin Bargu na shidda (6), Aliyu Buhari (1914 – 1947); Sarkin Bargu na bakwai (7), Abdullahi Aliyu (1947 – 1960); Sarkin Bargu na takwas (8), Umaru Aliyu (1960 – 1967); Sarkin Bargu na tara (9), Bello Aliyu (1967 – 1973); Sarkin Bargu na goma (10), Ahmadu Aliyu (1973 – 1995); Sarkin Bargu na sha daya (11), Shehu Aliyu (1995 – 2006); sai kuma Mahaifin Sarkin Bargu na sha ukku (13), Mustapha Usman, watau Sarkin Bargu na sha biyu (12) Usman Adamu (2006 – 2021).

Garin Ka’oje, wanda gunduma ce a cikin Karamar Hukumar Mulki ta Bagudo, ta ci gaba da habaka a karkashin Masauratar Gwandu.

Ilahirin ‘ya ‘yanta sun sami fice da daukaka a wurare da dama a cikin Nijeriya da kuma kasashen waje. Duniya tana ganin kimar garin Ka’oje saboda ‘ya ‘yanta, maza da mata, dake taimakawa a fannoni da dama na aikin zamani, a ko ina cikin kasar Nigeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *