Mutanen Dambatta, Makoda sun yaba wa Injiniya Saleh Wailare

Mutanen Dambatta, Makoda sun yaba wa Injiniya Saleh Wailare

Mutanen Dambatta, Makoda sun yaba wa Injiniya Saleh Wailare

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Al’ummar kananan hukumomin Dambatta da Makoda sun nuna godiyar su  ga Injiniya Saleh Musa Wailare, saboda abubuwa na alheri da yake yi a yankin tun lokaci mai tsawo ba tare da nuna gajiyawa ba.

A wata ganawarsu da wakilinmu, mutanen kananan hukumomi biyu wadanda kuma suka kasance mazabar tarayya sun bayyana Injiniya Saleh Musa Wailare a matsayin jarumi wanda kuma yake kaunar taimak awa mutane duba da irin yanayin da ake ciki na zamantakewa da kuma rayuwa a wannan lokaci.

Malam Ahmadu Shankate da  Malam Salihu Dan Marke da kuma Malama Hajara Kadandani daga yankin karamar hukumar Makoda sun sanar da cewa, Injiniya Saleh Wailare yana matukar kokari wajen tallafa wa al’umma ta kowane fanni duk da cewa, baya cikin shugabanni da aka zaba amma domin ya taimaki al’umma a kankin kansa.

Sannan sun kara da cewa, abin da Injiniya Wailare yake, ya zaburar da su  domin su yi waiwaye wajen irin mutanen da za su sanya a gaba idan zabe ya zo, musamman ganin cewa, shugabanni zababbu sun gaza wajen taimakon al’umominsu sai idan zabe ya matso kawai suke neman jama’a domin biyan bukatun su na siyasa.

A yankin karamar hukumar Dambatta kuma, mutanen da suka tattauna da Albishir sun danganta Injiniya Saleh Musa Wailare da cewa, yana da manufofi masu kyau wadanda kuma ake alfahari da su, a matsayinsa na mai kishin al’umma ba tare da nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi ba, inda kuma suka jaddada cewa, sun gamsu da yadda Injiniyan yake tafiyar da al’amuransa na taimaka wa al’umma.

Wani matsahi da ke garin Gwarabjawa Nura Adamu yace, babu shakka matasan kananan hukumomin Dambatta da  Makoda sun yaba da kokarin Injiniya Wailare musamman ta fuskar taimaka wa fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma bayar da kayan abinci mai tarin yawa domin ci gaba da ibadar azumi cikin jin dadi.

Sannan ya  bayyana cewa, matasan za su fara wani aiki na isar da manufofin Injiniya Saleh Musa Wailare a dukkan mazabu da manyan garuruwan da ke karkashin wannan mazaba ta tarayya,  wadda ta hada Dambatta da Makoda ta yadda kowa zai fahimci cewa, shugabanci yana bukatar taimaka wa al’umma da kulawa da al’amuransu.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan lamarin, Injiniya Saleh Musa Wailare ya ce, taimaka wa al’umma shi ne babban abin da yake cikin zuciyar sa, sannan ya sanar da cewa mutanen kananan hukumomin Dambatta da Makoda duka nasa ne domin haka zai ci gaba da kokari bakin gwargwadon iko yaga al’umma suna samun taimakon sa ba tare da nuna son zuciya ba.

Sannan ya yi amfani da wannan dama wajen Isar da sakon fatàn alheri ga al’umomin  kananan hukumomin Dambatta da Makoda bisa zagayowar wata mai alfarma na Ramadan tare da fatan cewa za’a ci gaba da yin ibada cikin nasara da jin dadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *