Mutanen Nijeriya, a rungumi kaunar juna, Da’a ga shugabanni -Aujarawar Alkali

Sarkin Gaya

Sarkin Gaya

Tura wannan Sakon

Daga Salihu S. Gezawa

An yi kira ga al’ummar kasar nan kan su himmatu wajen nuna da’a da kaunar juna da kuma ci gaba da addu’o’i ga magabata da kokarin kiyaye hakkokin juna.

Kiran ya fito daga bakin Dagacin garin Aujarawar Alkali, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad (Ruwata) da ke karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano, a lokacin da yake mika sakon barka da Sallah ga al’ummar Musulmi Nijeriya.

Ya ce, akwai bukatar a kara fadakar da al’umma abin da suka sani na sada zumunci da kyautata zamantakewar juna. Alhaji Ruwata ya yi kira ga al’ummar Musulmi kan su zama tsintsiya madaurinki daya ta kowanne bangare, inda ya ci gaba da cewa, nuna halin kwarai da dattako na cikin kyawawan al’adu na Hausa/Fulani, da koyarwar addinin Musulunci.

Da ya juya ga mahukunta, Alhaji Ruwata kira ya yi a garesu da su rinka tausasawa na kasa, tare da mayar da hankali wajen taimakon al’umma ako da yaushe.

Alhaji Ruwata ya kuma mika sakonsa na barka da Sallah ga Maimartaba Sarkin Gaya, Alhaji Dokta Aliyu Ibrahim da Hakimin Gezawa kuma mai Unguwar Mundubawa, Alhaji Mahmud Aminu Yusufu, da wakilin Hakimi, Alhaji Kabiru Tanko da daukacin al’ummar karamar hukumar Gezawa, ya kuma gode wa daukacin talakawan kasarsa ta Aujarawar Alkali kan hadin kai da suke ba shi wanda shi ne kashin bayan ci gaban da suke samu.

Daga nan Alhaji ya yi roko ga gwamnatin jihar Kano karkashin ma’aikatar raya karkara da a kawowa hanyar garinsu dauki, daga titin Hadejia zuwa titin Larabar Abasawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *