Mutanen U/Dallatu, kada a bata rawa da tsalle -Anas Kaura

Matawalle ya zama jagoran APC a Zamfara

Bello Matawalle jagoran APC a Zamfara

Tura wannan Sakon

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau An bukaci al’ummar unguwar Dallatu da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara, da kada su bata rawan da tsalle bisa bukatar da suke da ita na gwamnati ta gina masu makarantar boko.

Hakan ya fito ne daga bakin mai baiwa gwamna shawara na musamman kan tsare-tsaren birane, Anas A. Kaura a lokacin da yake zantawa da manema labai a ofishinsa da ke Gusau .

Anas ya ce, ya ji mutanen unguwar Dallatu sun tayar da kayar baya domin sun ji gwamnati ta dauki wani mataki na maida wadansu ‘yan-kasuwa filin karamar hukumar Gusau. Ya kara da cewa, su wadanda za’a mayar da wurin za’a mayar da su ne na wani lokaci kafin a nema masu guri na dindindin, domin hakan take kira ga al’ummar unguwar da su mayar da wukar, kada su bata rawarsu da tsalle.

Kaura ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatin jihar tana sane da bukatarsu da suke nema, kuma nan ba da jimawa ba gwamnati za ta share masu hawaye, ya ce, kada su manta wannan filin da suke maganar a gina masu makarantar filin karamar hukumar Gusau ce. Al’ummar unguwar Dallatu da ke cikin birnin Gusau sun koka kan mayar da kananan ‘yan-kasuwa da ke kasuwanci a Dogon Gida da ’yan Gwangwani da ke kusa da fadar gwamnatin jihar daga matsuguninsu zuwa sakatariyar karamar hukumar Gusau da ke Unguwar, da gwamnatin jihar Zamfara ke shirin yi.

A zantawarsa da manema labarai shugaban al’ummar Unguwar Dallatu, Alhaji Bashiru Muhammed ya ce, tun da farko sun bukaci a mayar da sakatariyar da aka yi watsi da su zuwa makarantun firamare da karamar sakandire domin amfanin mazauna yankin, kuma mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammed Nasiha ya na sa ne .

Ya ce “Ya umarce mu da mu rubuta wata bukata dangane da bukatar mu na sauya sakatariyar karamar hukumar da ba a kammala ba, wanda muka yi , kuma muka mika bukatar mu ga karamar hukumar” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *