Na ci amanar ‘yan Nijeriya idan ban fito takara ba –Osinbajo

Na ci amanar ‘yan Nijeriya idan ban fito takara ba –Osinbajo
Tura wannan Sakon

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce, zai iya zama cin amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar APC.

Ya kuma ce, rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi, a wadansu lokatai, ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Nijeriya.

“Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Ikko ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba,” in ji Osinbajo.

A nasa bangaren, gwamna Akeredolu ya ce, duk da cewa, ‘yan deleget na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, Ubangiji ne kawai ke bayar da mulki.

Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban kasa a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan ‘yan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top