Na fito takara domin taimaka wa al’umma -In ji Mista lecturer

Malam Ridwanu Murtala watau Mista Lecturer

Tura wannan Sakon

Labarai daga Musa Diso

Wani fitaccen matashi dan kishin kasa kuma mai son ganin ci gaban al’umma, musamman matasa maza da mata, Malam Ridwanu Murtala watau Mista Lecturer ya ce, ya fito neman takarar dan majalisar jihar Kano daga yankin karamar hukumar Tudun Wada, domin ci gaban al’umma da bunkasar tattalin arzikin kasa da kuma samar da zaman lafiya ga jama’a.

Ya ce, tabbas babu wata kasa a duniya idan har al’umma suna cikin talauci rashin aikin yi da kuma rashin tsaro.

Mista Lecturer ya yi jawabin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano a makon da ya gabata. Ya ce, sanin kowa ne cewa, matasa su ne ginshikin ci gaban al’umma kuma babu wani abu da za a yi a fadin duniya ba tare da gundumawar matasa ba.

Saboda haka idan har ana son samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowace kasa dole a samar wa matasa aikin yi da ingantaccen ilimi da kuma uwa uba samar da harkar noma domin duk kasar da ba za ta iya ciyar da al’ummarta ba, tabbas akwai kalubale na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Malam Ridwanu ya ce, burinsa a nan idan har Allah ya tabbatar masa da takararsa shi ne yaga ya kawar da duk wani kalubale da ke hana ci gaban al’umma musamman ta wajen samar da ingantaccen ilimi da kuma rashin aikin yi ga matasa. Daga nan ya yi kira ga al’umma cewa, lokaci ya yi da za a samu canji wajen samar da ci gaban jama’a da makamantansu.

Daga karshe, ya yi kira ga jama’ar jihar Kano da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin ganin an zabi jam’iyar NNPP a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *