Na kashe makwbcina ba tare da niyya ba -In ji Hadiza Pulka

Hadiza Abdullahi

Hadiza Abdullahi

Tura wannan Sakon

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri

A ranar Larabar da ta gabata, wata mata ta bayyana cewa, ba da niyya ta kashe wani makwabcinta ba, bayan wata ‘yar hatsaniya da ta barke a tsakaninsu a kauyen Pulka da ke karamar hukumar Gwoza, a jihar Borno.

Wakilinmu ya rawaito cewa, Hadiza Abdullahi, mai shekaru 20, ta bayyana hakan ne a Maiduguri, babban birnin jihar, yayin wani taron manema labarai da rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta gudanar, tare da holin wasu mutane 86 da ake zargi da aikata laifuffuka da aka ce sun aikata daban-daban, da suka hada da kisankai da ta’addanci da kama laifin hada baki da sata da makamantan haka.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Abdu Umar, wanda ya bayyana cewa, har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar 8 ga Mayun wannan shekarar, lokacin da wadda ake zargin, Hadiza ta kashe makwabcinta da kwalba.

“ A cewar kwamishinan, “Marigayin ya mutu nan take, bayan faruwar lama`n”. Ya kara da cewa, “A ranar 8 ga Mayu, 2022, da misalin karfe 1400 na safe, wacce ake zargin, Hadiza Abdullahi, daga kauyen Pulka, karamar hukumar Gwoza, ta je wata rijiyar burtsatse da ke kusa da ita domin dibar ruwa, inda marigayin, Ali Ibrahim Male na wannan adireshin ya hana ta dibar ruwa.

“Sakamakon haka, wacce ake zargin, ta yi amfani da kwalba ta daba wa marigayin a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take,” in ji Umar. Hawaye na gangarowa a kuncinta, Hadiza wacce Uwar ‘ya’ya biyu ce; ta shaida wa manema labarai cewa, ba wai abin da ta yi ba ne don kashe marigayi Ibrahim, inda ta ce ta roki marigayin ne da ya ba ta damar debo ruwa domin ta yi wa ‘ya’yanta abinci.

Ta ce, “Na je diban ruwa a wata rijiyar burtsatse da ke kusa da gidana, a Pulka. Amma da isa wurin, marigayin ya ki ba ni dama in dibi rowan.” Ta ci gaba da cewa, “Na shaida wa marigayin cewa, ba ni da ruwan da zan yi wa ’ya’yana abinci, da sauran abubuwan amfanin gida, amma marigayin ya ki.

Daga nan na yanke shawarar jefar da bokitin da na zo diban rowan, wanda kafin ka ce kwabo, marigayin ya fusata ya buge ni a bayana da bokitin diban ruwan ya kuma mare ni.”

“A cikin haka ne sai ni ma na fusata, na waiwaya, na tarar da wata kwalbar da ta fashe wacce na jefa masa, amma abin takaici, hakan ya kai ga mutuwarsa.

Ban taba nufin in kashe shi ba, ina son iyayensa da gwamnati su gafarta mini su sake ni daga tsarewar da ake min a hannun ‘yan sanda.”

Daga nan sai kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, an sami jimillar kararraki 45 tun daga watan Mayu zuwa yau, inda ya kara da cewa, an riga an shigar da kararraki 10 a gaban kotu, yayin da aka kama mutane 87 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban`

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *