Na matsu na sauka daga shugabanci –Buhari

Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka

Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka

Tura wannan Sakon

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ya matsu ya ga ya sauka daga mulkin kasar, wanda ya bayyana a matsayin jagoranci mai cike da kalubale da wahalhalu a tsawon shekaru 7 da ya shafe yana rike da shi.

Shugaban ya bayyana haka ne, yayin ganawa da wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyarsa ta APC, wadanda suka ziyarce shi a Daura, inda yake hutun Sallar layya.

Yayin da yake kokawa kan yadda ayyuka suka hana shi sakata a cikin shekaru bakwai da suka gabata, shugaba Buhari ya shaida wa gwamnonin da sauran jagororin siyasar da suka ziyarce shi cewa kusan shekara guda bai je gidansa dake Daura ba, saboda bukatun ofishinsa.

Buhari ya kara da cewar mai martana Sarkin Daura Dakta Umar Faruka ne ya ja hankalinsa a filin Sallar Idi inda ya ce karo na karshe da ya ziyarci garin Daura shi ne lokacin Sallar layya ta shekarar bara.

Buhari ya kuma bayyana cewar nan da watanni goma zuwa sha daya, zai koma garin na Daura, duk da cewa yana da gida mafi kyau a Kaduna, sai dai zaman Kadunan yayi kusa da Abuja.

Dangane da kokarin gwamnatinsa, Shugaban Najeriyar ya ce jagorancinsa ya cancanci jinjina la’akari da yadda yayi kokarin aiwatar da ayyuka, musamman na samar da ababen more rayuwa, duk da kalubalen karancin kudaden tafiyar da ayyukan na yau da kullum saboda tasirin lamurra daban daban a matakin duniya da ya shafi kasashe irinsu na Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *