Nadamar Obasanjo kan Atiku: PDP ta yi barazanar fasa kwan

Tura wannan Sakon

Daga Wakilinmu

Jam’iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta mayar wa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo martani kan kalaman da ya yi cewa ya yi kuskure lokacin da ya zabi mataimakinsa a 1999.

A karshen makon da ya kare ne aka ruwaito Obasanjon na cewa ya yi kuskure wajen zabar wanda zai yi masa mataimaki kafin zaben na 1999.

A shekarar ta 1999 aka zabe shi shugaban kasa tare da dan takarar PDP na shugaban kasa na yanzu na zaben shekara mai zuwa 2023, Atiku Abubakar, a matsayin mataimaki. Kodayake tsohon shugaban bai ambaci Atiku ba a kalaman nasa, amma ya ce kuskure ne ya yi, amma da zuciya daya, wanda kuma Allah Ya kare.

A martanin nata PDP ta yi barazanar abin da ta kira tona asirin waye Obasanjo idan har bai fayyace abin da yake nufi da kalaman nasa ba cikin sa’a 48.

A wani taron manema labarai a Kaduna, jiya Litinin shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar ta PDP, Sanata Walid Jibril ya ce jam’iyyar tana mutunta tsohon shugaban kasar, saboda haka za ta yi mamaki a ce wadannan kalamai sun fito ne daga Obasanjo.

Ya kuma zargi tsohon shugaban da cewa yana jin haushin Atiku Abubakar ne saboda ya hana shi cimma burinsa na ta-zarce, duk kuwa da irin taimakon da tsohon mataimakin nasa ya bayar wajen cimma nasara a gwamnatin Obasanjon. Sanata Walid ya ce, ‘’Ko ma mene ne dai a yanzu Abubakar Atuku shi ne dan takararmu, kuma ina bayar da tabbacin cewa shi ne zai zama shugaban kasa a 2023, in-shaAllah.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *