NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin Hajjin bana

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sanar da kudin kujerar aikin Hajjin bana da kowa ne maniyyaci zai biya.

A sanarwar da shugaban hukumar, Alhaji Zukrullah Hassan ya sanar a ranar Asabar a Abuja, ya ce, kudin kujerar ya danganta da nisan Maniyyata.

Sanarwar ta ce, Alhazan da suka fito daga yankin kudancin Nijeriya, za su biya Naira miliyon 2,496,815.29, yayin da wadanda suka fito daga yankin Arewacin Nijeriya za su biya Naira miliyon 2,449, 607.89.
Sai kuma Wadanda suka fito daga jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira miliyon 2,408,197.89, saboda kusancin su da kasar Makka.a

Hukumar ta kuma bukaci Mahajjata da su yi gwajin cutar Korona a kan rangwamen kudi na Naira dubu 30.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, hukumar ta bukaci hukumar aikin Hajji ta kasar Makka da ta kara yawan maniyyata daga Nijeriya, kuma hukumar tana jiran amsa daga Saudiyya.

Ya kuma umarci hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su ci gaba da gudanar da aikinsu bisa abin da aka ware musu, maimakon jira a kara musu kaso.

Ya bayyana cewa, a yayin da ake shirin bizar jami’ai da mahajjata a cikin jirgin farko, ya kamata jihohi su fara sarrafa bizar ga dukkan nau’o’in maniyyatan da suka yi rajista.

Hassan ya kuma bayyana cewa hukumar shige da fice ta Nijeriya ta yi alkawarin taimaka wa jihohin da ke fama da matsalar samun fasfo na tafiye-tafiye ga maniyyata.

Hukumar NAHCON ta bukaci jihohi da su gaggauta kammala tura kudaden da ake tura wa alhazai domin gudanar da shirye-shirye cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *