Nakasassu sun yi barazanar kai karar INEC kotu

Nakasassu sun yi barazanar kai karar INEC kotu

Masu bukata ta musamman

Tura wannan Sakon

Masu bukata ta musamman a jihar Ekiti da ke kudancin Nijeriya sun yi barazanar kai hukumar zabe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan korafin kin tanadar abubuwan da suke bukata domin shiga zaben gwamna da za a yi ajihar ranar 18 ga watan Yuni.

Jaridar Premium Times ta ambato shugaban kungiyar masu bukata ta musamman reshen jihar Ekiti, Dabid Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa, matukar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da kara kotu kan take hakkinsu, da dokokin Nijeriya suka ba su a matsayin ‘yan kasa.

Mr Anyaele ya kara da cewa, “duk wani yunkuri na hana ‘ya’yan kungiyarmu kada kuri’a zai sa mu kalubalanci INEC a gaban kuliya domin take dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu kan walwalarmu.”

Ya kara da cewa, kungiyarsu ta damu matuka kan halin tabarbarewar tsaron da ake fuskanta, musamman yadda ‘yan daba ke hana wadansu kada kuri’a. Domin haka ya bukaci hukumar zaben ta yi aikin hadin gwiwa da ‘yan-sanda domin ba su tsaron da ya dace a lokacin zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *