Nan Bada Jimawaba Za’aga Canji Wajen Gudanar Da Tsaro A Kasar Nan- AIG Bello

AIG AS BELLO

Tura wannan Sakon

Rabiu Sanusi daga Kano

An bayanna yunkurin hukumar Yansandan Nijeriya karkashin jagoranci Usman Baba wajen ganin ansamar da karin cigaba da tsaro da kayan aiki akasar nan.

Bayanin hakan yafito daga bakin mataimakin shugaban Yansandan mai wakiltar shiyyar Kano da Jigawa watau AIG Sadiq Abubakar Bello yayin taron kaddamar da manyan motoci guda biyu da shugaban Kamfani Triple K, Alhaji Najib Jafar Koguna yabama mopol lamba ta tara dake karamar hukumar Tarauni ajahar Kano.

AIG Sadiq Abubakar Bello yakuma kara dacewa a kokarin shugaban Yansanda nakasa wajen kara kawo canji wajen tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin al’umma.

Haka zalika yakuma Kara cewa yanada yakinin Mai girma shugaban Yan Sanda nakasa na aiki kan yadda zai kara samama jami’an Yan sanda gurin zama mai kyau da kayan aiki dan cigaba da bada himma wajen kare hakkin jama’ar kasar nan da rayukan mutane.

Sannan yakuma bukaci sauran masu hannu da shuni  na jahar Kano da Jigawa dasu Kara shigowa dan Kara taimakon jami’an tsaro da damar da allah yabasu dan ganin ansamu cigaba da zaman lafiya.

Kuma yaja hankalin jami’an dake kula da yanki na tara wajen ganin sunyi amfani da wannan motoci ta hanyar da ya dace tare da kula dasu yadda yakamata,sannan sukama samama masu direbobi nagari dan samu damar amfani dasu atsawon lokaci.

Shima Alhaji Najib Jafar Koguna yace lallai matsayin da Allah yabasu da damar dasuke da ita yakara jan hankali wajen sama masu motoci dan gudanar da aiki cikin sauki.

Alhaji Najib yakumace taimakon jami’an tsaro kamar ya taimaki al’ummar shine,Dan kuwa aikin jama’a ne da kasar nan dan haka ba wani abin wahala bane kowa yanada kyau taimaki jami’an tsaro musamman Yansandan suna matukar kokari wajen kare Al’umma da dukiyoyinsu.

Daga karshe yace nan bada jimawaba zasu kara gabatarma da zone one da heditkwata Suma  nasu motocin guda byu-biyu dan cigaba da gudanar da aikinsu na kare jama’a da dukiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *